Wani Sanata ya gwangwaje sarakan jiharsa da motocin alfarma 34

Wani Sanata ya gwangwaje sarakan jiharsa da motocin alfarma 34

- Sanata mai wakiltar jihar Taraba ta Kudu ya gwangwaje sarakunan yankin da motocin alfarma har 34

- Ya bayyana cewa, tsananin ganin girma da mutunta su ne yasa yayi hakan don suna kokarin hada kan al'umma

- Mataimakin gwamna jihar Taraba a bangaren yada labarai ya musanta rade-radin da ake na cewa gwamnan ya hana sarakunan karbar motocin

Sanata mai wakiltar jihar Taraba ta Kudu a majalisar dattijai, Sanata Emmanuel Bwacha ya rarraba motocin alfarma 34 ga sarakunan gargajiya dake yankin jihar Taraba ta Kudu.

An rarraba motocin ne a yayin wani bikin murnar Wukari wanda ya samu halartar sarakunan gargajiyar yankin.

Sanata Bwacha ya ce ya samar da ababen hawan ne ga sarakunan gargajiyar, saboda nuna girmamawa tare da mutunta masarautun gargajiyar.

Ya jinjinawa sarakunan gargajiyar sakamakon rawar da suke takawa wajen habaka zaman lafiya, da hadin kai ga mabiyansu a duk yankin da suke shugabanta.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Zamfara ta dau tsautsauran mataki a masu satar shanu

A hakan ne kuma mataimakin gwamna Darius a fannin yada labarai, Bala Danabu ya musanta zargin da ake yadawa a kafafen sada zumunta na cewa Gwamna Darius ya hana sarakunan karbar wannan tagomashin arzikin da Sanata Bwacha ya bada.

Bala Danabu ya ce wannan labari ne na karya kuma kirkirarre, maras tushe balle makama. Hakazalika Gwamna Darius bai hana sarakunan karbar wadannan motocin ba.

Jaridar Daily Trust ce ta gano yadda Sanata Emmanuel Bwacha ya rarraba motocin kirar Highlander da sauran kasaitattun motocin ga sarakunan dake yankin Kudancin jihar Taraba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel