Majalisar kasar Amurka za ta karrama Sowore

Majalisar kasar Amurka za ta karrama Sowore

- An zabi mawallafin jaridar Sahara Reporters don karbar kambun girmamawa daga Amurka

- Dan majalisar Amurka, Josh Gottheimer ne ya zabi mai rajin kare hakkin dan Adam din don karbar lambar yabon

- Shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta Tom Lantos ce za ta mika lambar yabon don habaka kare hakkin dan Adam a duniya

Omoyele Sowore, mawallafi a jaridar Sahara Reporters kuma shugaban shirin juyin juya hali na #RevolutionNow an zabesa don karramawa a kasar Amurka, a matsayin fursunan Amurka na shekarar 2019.

Hakan ya biyo bayan garkamesa na tsawon lokaci da hukumar jami’an tsaron farin kaya na Najeriya tayi na tsawon lokaci sannan ta kara damkesa bayan da kotu ta bada umarnin sakinsa.

Kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta bayyana, za a ba Omoyele Sowore kambun yabon ne daga hukumar kare hakkin dan Adam ta Tom Lantos dake majalisar wakilan kasar Amurka.

DUBA WANNAN: Gwamnatin jihar Zamfara ta dau tsautsauran mataki a masu satar shanu

An saki mawallafin ne bayan da ministan tsaro na Najeriya, Abubakar Malami ya bada. Hakan ya kuwa jawo wa Malami jinjina da yabo a fadin kasar nan saboda jajircewarsa ta gyara kasar.

An gano cewa, hukumar kare hakkin dan Adam ta Tom Lantos dake majalisar wakilan kasar Amurka ta kware ne wajen habakawa, karewa da kuma tallata kare hakkin dan Adam a fadin duniya.

Gottheimer ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da kare Sowore da samar da yanayi mai kyau ta yadda zai samu iyalansa cikin koshin lafiya.

“Zamu cigaba da lura da al’amuran dake faruwa a Najeriya, damokaradiyya ce da take da kusanci da Amurka, don haka dole mu tabbatar da gwamnati ta mutunta dokokin kare hakkin da Adam,” in ji dan majalisar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel