Wata sabuwa: Kungiya ta nemi gwamnatin tarayya ta kyale karuwai su fara rijista a Najeriya

Wata sabuwa: Kungiya ta nemi gwamnatin tarayya ta kyale karuwai su fara rijista a Najeriya

- Wata kungiya mai zaman kanta a Najeriya ta bukaci majalisar tarayyar Najeriya da ta bari karuwai su fara rijista a Najeriya

- Kungiyar ta bayyana cewa bawa karuwan damar rijista zai kawowa Najeriya wata hanya da za ta dinga samun kudin shiga

- Haka kuma shugaban kungiyar ya kara da cewa gwamnatin za ta iya fito da wata hanya da za ta dinga sanyawa karuwan doka kafin ayi musu rijista

Kungiyar TDAGRI mai zaman kanta dake Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta bar karuwai su fara rijista a Najeriya.

Shugaban kungiyar, Hon. Nebeck Eziora shine ya bukaci hakan a wata sanarwa da ya fitar mai suna, ‘Najeriya a mahangar cigaba a fannin siyasa’.

Shugaban ya bukaci gwamnatin ta bari karuwai su fara rijista a matsayin kasuwanci, domin hakan ma wata hanya ce da kasa za ta dinga samun kudaden shiga ta bangaren su.

Ya kuma bukaci gwamnati ta fito da wata hanya da za ta dinga lura da yadda karuwan suke tafiyar da al’amuransu.

KU KARANTA: Yadda mijina yayi kokarin yanke kai na dana 'ya'yanmu domin yin asiri damu

Haka kuma Eziora ya bayyana wasu hanyoyi da gwamnati za ta bi wajen sanya doka a harkar karuwancin, inda suka hada da: duk wacce ke son shiga harkar sai ta yanki fom da hukumar kula da kamfanoni ta Najeriya ‘Cooperate Affairs Commission’ a turance, haka kuma dole ta kawo mutane uku amintattu a wajenta, ciki kuwa hadda Sarkin garinsu ko Mai Gari, da kuma iyayenta.

A cewar Hon. Eziora, yanzu haka sun aikawa da majalisa wannan bukata ta su domin su sanyata ta zama doka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel