Zan yi bajinta fiye da na gwamnatin baya – Gwamnan Bauchi

Zan yi bajinta fiye da na gwamnatin baya – Gwamnan Bauchi

- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammed ya ba mutanen jihar tabbacin cewa yana aiki ba dare ba rana domin yi masu aiki

- Ya sha alwashin nuna bajinta wajen yiwa jihar hidima fiye da na gwamnatin baya

- Ya ce gwamnatinsa ta jajirce don ganin ta kafa tarihi mai kyau duk da cewar ta gaji matsaloli da dama wanda ya shafi ma’aikatu daban-daban na tattalin arziki a jihar

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ba mutanen jihar tabbacin cewa yana aiki ba dare ba rana domin yin aiki fiye da na gwamnatin da ya gada.

Gwamna Muhammed ya bayar da tabbacin ne a jiya Alhamis lokacin da ya karbi bakuncin jami’an kungiyar kiristocin Najeriya reshen jihar, wadanda suka kai masa ziyarar Kirsimeti a gidan gwamnati a Bauchi.

Ya ce gwamnatinsa ta jajirce don ganin ta kafa tarihi mai kyau duk da cewar ta gaji matsaloli da dama wanda ya shafi ma’aikatu daban-daban na tattalin arziki a jihar.

Gwamnan ya yi kira ga al’umman Kirista da su yi amfani da damar bikin Kirsimeti wajen wanzar da aminci sannan ya mika godiya gare su kan tarin goyon bayan da suka bashi lokacin gudanar da zaben gwamna da aka yi.

Da suke mayar da martani, Shugaban CAN, Reverend Joshua Ray Maina, ya gwamana tabbacin samun cikakken goyon bayanansu ta hanyar addu’o’i domin cimma nasara a gwamnatinsa.

KU KARANTA KU KARANTA: Mutane 9 sun mutu, 100 na kwance rai a hannun Allah, bayan sun dirki barasa mai guba

Faston ya yi godiya ga gwamnan kan daukar nauyin kiristoci 110 domin yin ibadah.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel