Malam El-Rufai ne kadai ke da hurumin sakin Sheikh Zakzaky – gwamnatin tarayya

Malam El-Rufai ne kadai ke da hurumin sakin Sheikh Zakzaky – gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa gwamnatin jahar Kaduna a karkashin jagorancin Malam Nasir Ahmad El-Rufai ce kadai za ta iya sakin shugaban kungiyar yan Shia ta yan uwa Musulmi, Sheikh Ibrahim Zakzaky.

Jaridar The Nation ta ruwaito ministan sharia, kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, 27 ga watan Disamba, inda yace ana tuhumar Zakzaky a karkashin dokokin jahar Kaduna ne ba dokokin tarayya ba.

KU KARANTA: Magu na fuskantar sabon tarnaki game da tabbatar da shi shugaban EFCC mai cikakken iko

Malami yace sharia’ar Zakzaky ba daidai take a shari’ar Sambo Dasuki da Omoyele Sowore ba, mutane biyun da gwamnatin tarayya ta sake su a ranar Talata, 24 ga watan Disamba bayan kwashe tsawon lokaci a hannu.

“Idan har ana tuhumar wanda ake zargi da aikata laifi a karkashin dokokin jaha ne, toh umarnin kotu na bayar da belinsa ya rataya ne a kan gwmanatin jaha, haka zalika idan ana tuhumar wanda ake zargi da aikata laifi a karkashin dokokin gwamnatin tarayya ne, umarnin kotu na bayar da belinsa na kan gwamnatin tarayya.” Inji shi.

Idan za’a tuna, Zakzaky da matarsa Zeenah sun shiga hannu ne tun bayan arangama da aka yi da Sojoji da yan Shia a wata Disamba na shekarar 2015 yayin da yan Shian suka tare ma babban hafsan sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai hanya a garin Zaria.

Sai dai duk umarnin da wata kotu ta bayar a watan Disambar 2016 na sakin Zakzaky da matarsa, gwamnati ta ki sakinsa, inda a ranar 18 ga watan Afrilun 2018 gwamnatin jahar Kaduna ta maka shi gaban kotu tana tuhumarsu a kan laifuka 8.

A wani labarin kuma, jim kadan bayan fitowarsa daga hannun hukumar DSS, mashawarcin tsohon shugaban kasa Jonathan a kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki ya bayyana cewa a shirye yake ya fara kare kansa a gaban kotu.

Gwamnati na zargin Dasuki da laifin mallakar miyagun makamai ba tare da ka’ida ba, tare da hannu cikin badakalar kudi naira biliyan 35 da kuma satar kudin makamai dala biliyan 2.1 da aka ware domin sayen makamai.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel