Gwamnatin jihar Zamfara ta dau tsautsauran mataki a masu satar shanu

Gwamnatin jihar Zamfara ta dau tsautsauran mataki a masu satar shanu

- Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da sabuwar dokarta ta hana siyar da shanu babu rubutacciyar shaida da hoto

- Kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar ya ce, anyi hakan ne don shawo kan matsalar satar shanu

- Gwamnatin ta kafa dokar hana shige da fice a jihar daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe

Gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da haramcin siyar da Shanu a jihar ba tare da shaida a rubuce ba da kuma hotuna.

Kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida na jihar, Abubakar Daura wanda ya sanar da wannan cigaban, ya ce an yanke wannan hukuncin ne don shawo kan yawan satar dabbobi da ake yi a jihar.

Tunawa da yadda tireloli biyar na shanu da aka sato a jihar Zamfara wadanda aka kama a Kaduna da jihar Legas, Daura ya ce jami’an tsaro a jihar sun hada runduna wacce zata dinga tantance shaidar shanun kafin a mika su ga masu siye.

DUBA WANNAN: Tsarin iyali ita ce hanyar shawo kan almajiranci - Sarki Sanusi

Ya ce: “Muna ta samun rahoto kala-kala na satar Shanu kuma jihar ta samo shanun sata 500 ta hanyar kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa a kan matsalolin tsaron. Gwamnatin jihar ba zata lamunci siyar da shanu ba, ba tare da shaida daga wata kasuwa a jihar.”

“Mun gabatar da hakan ne don mu samun sauki wajen gano masu siyar da shanun sata da kuma masu siya ta yadda zamu kamasu.” in ji shi.

Kwamishinan ya kara da bayyana cewa gwamnatin ta kafa dokar cewa, babu wani abun hawa da zai shiga ko fita daga jihar bayan karfe 6 na yamma ko kafin karfe 6 na safe.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel