Magu na fuskantar sabon tarnaki game da tabbatar da shi shugaban EFCC mai cikakken iko

Magu na fuskantar sabon tarnaki game da tabbatar da shi shugaban EFCC mai cikakken iko

A yanzu haka wasu hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari guda biyu sun shiga cikin jerin masu muradin kawar da Ibrahim Magu daga mukamin shugabancin hukumar EFCC tare da maye gurbinsa idan hakan ya tabbata.

Jaridar The Nation ta ruwaito baya ga barazanar da hadiman shugaba Buhari ke yi ma kujerar Magu, wani fitaccen gwamna daga yankin Arewacin Najeriya, kuma mai fada a ji ya janye goyon bayan da yake yi ma Magu sakamakon binciken lalitar jahar da EFCC ke yi.

KU KARANTA: Boko Haram ta kashe kiristoci 11 da ta kama a Borno a ranar bikin Kirismeti

Sai dai wasu masu neman ganin an kawar da Magu a fadar Aso Rock Villa sun nemi Buhari ya yi masa irin ta Nuhu Ribadu, ma’ana a tura shi karo karatu a cibiyar horas da manyan jami’an gwamnati dake Kuru, Jos, kamar yadda marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua ya yi ma Ribadu a 2007, sa’annan ya rage masa girma zuwa mataimakin kwamishinan Yansanda, daga karshe suka sallameshi daga aikin dansanda.

Amma duk da wadannan shawarwari, shugaban kasa Buhari ya gagara yanke takamaimen matakin da zai dauka game da Magu, wannan shi ne daliin da yasa har yanzu gwamnati ba ta sake mika sunansa ga majalisar dattawa domin tabbatar da shi mukamin ba.

Idan za’a tuna, Buhari ya taba tura sunan Magu gaban majalisa ta 8 da ta gabata domin a tantance shi har sau biyu, amma a karon farko, hukumar tsaro ta DSS da hadin bakin shugabanta Lawal Daura suka yi masa kafar angulu, a karo na biyu kuma majalisar ta bayyana rashin amincewarta da Magu.

Wata majiya daga Villa ta bayyana ma majiyar Legit.ng cewa: “Baya ga hadimna shugaban kasa guda biyu, akwai wasu manyan jami’an Yansanda guda hudu dake neman kawar da Magu, babu ruwansu da nasarorin da Magu ya samu a shugabancinsa.

“Kuma kasan Magu dan talaka ne, kuma bashi da wata sanayya da manyan mutane, musamman duba da irin aikinsa, don haka Allah kadai zai taimaki Magu ya cigaba da zama a kujerar nan, sai kuma shugaba Buhari.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel