Tsarin iyali ita ce hanyar shawo kan almajiranci - Sarki Sanusi

Tsarin iyali ita ce hanyar shawo kan almajiranci - Sarki Sanusi

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi a ranar Alhamis ya yi kira ga 'yan Najeriya da su haifa yawan ‘ya’yan da zasu iya kula dasu. Hakazalika su auri iyakar yawan matan da zasu iyawa adalci.

Sarkin ya bada wannan shawarar ne a bikin bude wani taron IVC karo na 108 wanda kungiyar musulmai ta Najeriya ta shirya a sansanin IVC na dindindin dake kan babban titin Legas zuwa Ibadan a jihar Ogun, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Basaraken ya jaddada cewa, matsalar almajiranci da ake samu a Najeriya ba matsalar addini bace, da kanmu zamu iya shawo kanta don tana ci wa mutane tuwo a kwarya a arewacin Najeriya.

Kalubalen almajirancin sun hada da: Kananan yara da basu zuwa makaranta wadanda iyaye ke mika wa malamai, amma kuma su bige da bara a titunan fadin kasar nan. Akwai miliyoyin kananan yara dake almajiranci a fadin kasar nan duk da kokarin gwamnati don shawo kan wannan matsalar.

A yayin da yake jaddada cewa, akwai bukatar a mayar da yaran makaranta, Sanusi ya ce akwai bukatar maza su dinga auren yawan matan da zasu iya rikewa.

DUBA WANNAN: Jigo a APC ya yabawa Buhari kan nasarorin da ya samu a zabe, tattalin arziki da tsaro

“Idan muka cigaba a haka, akwai yuwuwar kashi 40 na mutane ba zamu haifa n Najeriya zasu fada tsananin talauci. Talauci a Kudu maso yamma ya kai kashi 20, a Arewa kuwa kashi 80 ne, Legas na da kashi 8 amma jihar Zamfara kashi 91 ne.” ya ce.

Ya kara da cewa, “Munata kokarin shawo kan matsalar almajiranci, a kan me mutane zasu haifa ‘ya’yan da ba zasu iya kula dasu ba? Adalci garesu da kanka shine idan zaka iya kula dasu. A maimakon haihuwar ‘ya’ya da yawa, me zai sa ba zamu haifa yawan wadanda zamu iya kula dasu ba? Da yawa daga cikin yaran kan koma bangar siyasa ko yawo a titi saboda rashin kula.”

“Wannan ce shawarata a kan yawan tara yara. Ba matsalar addini bace, matsala ce a tsakaninmu wacce zamu iya shawo kanta da kanmu.” Ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel