Mutane 9 sun mutu, 100 na kwance rai a hannun Allah, bayan sun dirki barasa mai guba

Mutane 9 sun mutu, 100 na kwance rai a hannun Allah, bayan sun dirki barasa mai guba

- Mutane tara ne suka rasa ransu bayan da suka sha wata burkutun kwakwa da aka hada a gida

- A kalla sama da mutane 100 ne suke kwance a asibiti bayan da suka sha daga burkutun a wajen liyafar

- Wasu daga cikin mutanen sun fadi suna amai da mugun ciwon ciki inda wasu suka yi doguwar suma

Mutane tara ne suka rasu inda sama da mutane 100 ke kwance a gadon asibiti bayan da suka sha wata burkutu. A ranar Litinin ne wannan lamarin ya faru a kasar Philippine bayan da mutanen suka sha wata burkutun kwakwa suka fadi rai a hannun Allah.

Mutanen sun rasu ne bayan da suka sha burkutun da aka hada a gida mai suna Lambanog a wata liyafa a birnin Rizal dake yankin Laguna, mai nisan kilomita 70 daga kudancin Manila, kamar yadda rahoton ‘yan sanda ya nuna.

A kalla mutrane 122 ne aka hanzarta kaiwa asibiti daga birnin bayan da mugun ciwon ciki da amai ya kama su. Wasu daga ciki sun fadi basu san inda kansu yake ba.

KU KARANTA: Fada da aljani ba dadi: Barayi sun dawo da kayan da suka sata bayan sunji ruwan asiri

Mutum na karshe da ya rasu shine wanda ya fadi a birnin Candelaria a yankin Quezon a ranar Lahadi, kwanaki uku bayan da ya sha daga wannan burkutun da makwabta suka hada.

A wannan birnin ne kuma aka garzaya da mutane shida asibiti tare da wasu biyun da suka yi doguwar suma, kamar yadda rahoton ‘yan sanda ya bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel