Matsa wa kiristoci a Najeriya: Sultan ya maida wa CAN da martani

Matsa wa kiristoci a Najeriya: Sultan ya maida wa CAN da martani

Sarkin Musulmi kuma Sultan na Sokoto, Alhaji Abubakar Sa’ad ya nuna bakin ciki kan bayanan da kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) tayi na cewar wai Musulmai na matsa wa kiristoci a kasar.

A cewar Sultan hakan bai dace ba a ce wai kungiyar CAN na furta irin wadannan kalamai a kasar.

Har ila yau ya bayyana cewa ko “koke-koken da ake na cewa wai Fulani na halaka mutane a wasu yankunan kasar lallai a kwana da sanin cewa rikice-rikicen ba na addini bane.

“Idan har akwai zancen muzgunawa ya kamata ace CAN ta gabatar da wannan zamcen teburin tattaunawa da muke yi a tsakaninmu a lokuta da dama don a San matakin dauka a kai amma ba yin irin wannan zantukan ba saboda Amurka ta fadi hakan a rahotonta."

Kasar Amurka dai ta bayyana a rahotonta cewa Najeriya na daga cikin kasashen da ake matsa wa kiristoci.

KU KARANTA KUMA: Bikin Kirsimeti: Oshiomhole ya bada wa Gwamna Obaseki kasa a ido

Kungiyar CAN ta yi na’am da wannan rahoton inda ta jadadda cewa shakka babu ana muzguna wa kiristocin kasar.

Sultan ya bayyana haka a taron kungiyar Dalibai musulmai na jami’ar Bayero da ke Kano.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel