Sakon Kirsimeti da Sardauna ya aika wa Kiristocin arewa a 1959

Sakon Kirsimeti da Sardauna ya aika wa Kiristocin arewa a 1959

A yayin da shugabanni da jagorori ke cigaba da aka sakon taya Kiristoci murnar zagayowar ranar bikin Kirsimeti na shekarar 2019, Legit.ng ta yi wawaye 'adon tafiya' domin kawo sakon taya murna da firaministan yankin arewa, marigayi Ahmadu Bello, ya aika wa Kiristocin arewa a shekarar 1959.

A rubutaccen sakon na Sardauna ya bayyana cewa, "mutane ne mu da muka fito daga kabilu, addinai da al'adu daban-daban, amma kuma zaman tare ya hada mu wuri guda domin zama a matsayin al'ummar kasa daya.

"Duk da muna da banbance a hanyoyi da dama, abubuwan da suka hada mu zama wuri guda sun fi wadanda suka banbanta mu.

"A duk lokaci irin wannan, na kan yiwa jama'a tuni a kan bukatar mu kasance masu hakuri da juna saboda banbancin addinin dake tsakaninmu.

"Bamu da wata manufa ta nuna fifiko ga wani addini fiye da wani, jama'a kan iya dogaro ga wannan tabbaci da na bayar.

"Zamu kare mutuncin duk wani addini da mabiyansa matukar babu saba wa dokokin kundin tsarin mulki, a bisa dogaro da haka nake mika sakon taya murna, amadadina da na ministocina, ga mabiya addinin Kirista a wannan babbar rana.

"Lokaci ya yi da zamu jingine banbancinmu na addini a gefe domin mayar da hankali tare da hada kai wajen samun cigaban kasarmu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel