Aisha Buhari ta raba kayan alheri ga manyan asibitoci 4 a Kaduna

Aisha Buhari ta raba kayan alheri ga manyan asibitoci 4 a Kaduna

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari Halilu ta yi rabon kayan abinci gag a mabukata a wasu manyan asibitoci guda hudu dake fadin jahar Kaduna a matsayin tallafi ta karkashin gidauniyarta, Aisha Buhari Foundation, ABF.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito hadimi na musamman ga uwargidar shugaban kasa, Aliyu Abdullahi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamba a garin Abuja.

KU KARANTA: Na shirya tsaf domin kare kaina daga zargin satar kudin makamai – Sambo Dasuki

Aliyu yace daga cikin asibitocin da suka samu tallafin akwai asibitin St Gerald, asibitin FOMWAN, Barau Dikko da kuma babban asibitin Rigasa.

Da take raba kayan a madadin gidauniyar, hadimar uwargidar shugaban kasa Zainab Ikaz-Kassim ta bayyana cewa manufar raba kayan abincin shi ne domin tallafa ma marasa karfi da gajiyayyu marasa lafiya.

Malama Ikaz ta kara da cewa Aisha Buhari ta dade tana damuwa da duk abin da ya shafi lamarin gajiyayyu musamman mata da kananan yara.

Ita ma a nata jawabin, uwargidar gwamnan jahar Kaduna, Ummi El-rufai, yayin da ta karbar kayan a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, ta yaba da kokarin Aisha Buhari, sa’annan ta bayyana farin cikinta da yadda take damuwa da mawuyacin halin da talakawa ke ciki. Haka zalika Ummi ta bayyana godiyarta ga Aisha Buhari da ta zabi jahar Kaduna don raba wannan tallafi.

Kwamishiniyar kiwon lafiya ta jahar Kaduna, Amina Mohammed da kanta ta jagoranci zuwa rabon kayayyakin a asibitocin guda hudu, ita ma ta bayana farin cikinta tare da jaddada goyon baya ga duk ayyukan bayar da tallafi daya fito daga wajen Aisha Buhari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel