Bikin Kirsimeti: Oshiomhole ya bada wa Gwamna Obaseki kasa a ido

Bikin Kirsimeti: Oshiomhole ya bada wa Gwamna Obaseki kasa a ido

Kwamrad Adams Oshiomhole, Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma tsohon gwamnan jihar Edo, ya ki amsar kyautar Kirsimeti daga gwamnatin jihar.

Mista Crusoe Osage, mai ba gwamnan jihar shawara na musamman a kafofin watsa labarai ne ya bayyana hakan a jiya Laraba, 25 ga watan Disamba a Wani jawabi a Benin.

Osagie ya ce an dawo da kyaututtukan kayan Kirsimeti da aka turawa Oshiomhole.

Ya bayyana cewa an tura tawaga daga gwamnatin jam’iyyar har domin isar da kyautar a yammacin ranar Kirsimeti.

“Yan aiken sun ce sun tarar da mahaifiyar tsohon gwamnan wacce ta ki amsar kayayyakin, inda ta bayyana cewa danta ba zai amshi kyautar ba.

“Kyaututtukan sun hada da shanaye hudu da buhuhunan shinkafa 10.”

Ya ce rabon kayayyakin Kirsimeti abune da gwamnatin jihar ta saba duk shekara a matsayin hanyar nuna so da karfafa zumunci tsakanin gwamnatin da mutane.

Ya ce anyi rabon kayayyakin ga sauran ma’aikatan gwamnati da masu mukaman siyasa, shugabannin hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya, shugabannin addini da shugabannin makarantu da sauran manyan mutane a yankin.

Osagie ya ce Obaseki da Oshiomhole sun fada rikicin siyasa kan manufar gwamnan na mayar da hankali kan mayar da hankali ya jin dadin mutane sama da komai domin yana adawa da ba yan siyasa filin raba mu kashe da kudin jihar.

KU KARANTA KUMA: Ya kamata Buhari ya tsare Gwamnan CBN - Lamido

Ya ce gwamnan ya ajiye rikicin siyasa domin isar da aikinsa na aikawa Oshiomhole kyaututtuka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel