Cin zarafin mata: Yansanda sun kama wani Magidanci da laifin kashe matarsa

Cin zarafin mata: Yansanda sun kama wani Magidanci da laifin kashe matarsa

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jahar Ogun sun sanar da kama wani magidanci dan shekara 37, Mutiu Sonola a kan lafin lakada ma matarsa, Zainab dan banzan duka da ya yi sanadiyyar mutuwarta har lahira.

Mai magana da yawun Yansandan jahar Ogun, Abimbola Oyeyemi ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis, 26 ga watan Disamba, inda yace sun kama Mutiu a ranar Laraba ne bayan mahaifinta ya kai musu rahoton lamarin.

KU KARANTA: Duk sunan da za ku kira ni da shi baya damu na – Buhari ga yan Najeriya

“Mahaifin Zainab ne ya kai rahoto a ofishin Yansanda na Ibara a kan cewa an kirasa ta wayar salula an bayyana masa cewa diyarsa ta samu sabani da mijinta wanda ya kai ga ya lakada mata dan banzan duka har ta fita hayyacinta.

“Ya kara da cewa ba tare da bata lokaci bay a garzaya gidanta inda ya dauketa ya mikata zuwa babban asibitin Ijaye, inda a can ne likitoci suka tabbatar da mutuwarta.” Inji mai magana da yawun Yansanda.

Jami’in Yansandan yace a lokacin da magidancin ya gano matarsa ta mutu, sai ya ranta ana kare, amma duk da haka Yansanda sun samu nasarar cafko shi daga mabuyarsa, ya kara da cewa binciken farko ya tabbatar da mutumin ya saba jibgar matarsa.

Daga karshe kaakakin yace tuni sun mika gawar matar zuwa dakin ajiyan gawarwaki domin gudanar da bincike a kan gawarta tare da gano musabbabin mutuwarta.

Haka zalika kwamishinan Yansandan jahar Ogun, Kenneth Ebrimson ya bayar da umarnin mika Sonola zuwa sashin binciken manyan laifuka na rundunar Yansandan jahar domin gudanar da cikakken bincike a kansa tare da gurfanar da shi gaban kotu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel