Duk sunan da za ku kira ni da shi baya damu na – Buhari ga yan Najeriya

Duk sunan da za ku kira ni da shi baya damu na – Buhari ga yan Najeriya

Ko a jikina, wai an tsikari kakkausa, wannan shi ne manufar jawabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi ga tawagar jama’a yan asalin garin Abuja a karkashin jagorancin ministan babban birnin tarayya Abuja, Mohammed Bello a Villa.

Ministan tare da jama’an Abuja sun kai ma shugaban kasa ziyarar barka da kirismeti ne a fadar gwamnatin tarayya Aso Rock Villa a ranar Laraba, 26 ga watan Disamba don murnar kirismeti.

KU KARANTA: Mutane 2 sun mutu a harin da yan bindiga suka kai garuruwan jahar Kebbi

A jawabinsa, shugaba Buhari ya bayyana musu cewa duk abin da za’a fada game da shi ko kuma duk sunan da za’a kira shi, hakan ba zai sanya shi damuwa ba, saboda ba zai fasa riko da kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 ba.

Jaridar Punch ta ruwaito shugaba Buhari ya karbi bakuncin mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo kafin ziyarar jama’an Abujan, inda Osinbajo ya mika masa katin gaisuwa na murnar bikin Kirismeti da kuma sauran kayan kyaututtuka.

Da yake bayyana godiyarsa ga Osinbajo, Buhari yace gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen samar da ababen more rayuwa ga yan Najeriya, musamman tituna, lantarki da layin dogo ba tare da la’akari da maganganun masu magana ba.

A cewarsa: “Idan ka samar ma yan Najeriya da manyan ababen more rayuwa, ka gama dasu, kowa zai yi harkar gabansa ne kawai, ba zasu taba damuwa da wanene a gwamnati ba, amma idan ka hanasu ababen more rayuwa, toh lallai babu abin da zasu yi.”

Daga karshe ya sake nanata godiyarsa ga yan Najeriya da suka sake zabensa karo na biyu, inda yace yana sane da cewa dimbin jama’an da suka zabe shi basu zabe shi don kudi ba, domin kuwa ba zai iya biyansu ba, don haka yace ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen bauta ma Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel