Da mugun rawa: Jirgin Arik cike da fasinja ya yi juyin gaggawa saboda wata matsala

Da mugun rawa: Jirgin Arik cike da fasinja ya yi juyin gaggawa saboda wata matsala

- Wani jirgin kamfanin Arik Air, mai shawagi daga Lagas zuwa Port Harcourt a jiya Laraba, 25 ga watan Disamba ta yi dawowar gaggawa zuwa Lagas

- Hakan ya biyo bayan gano wata matsala a tattare da jirgin wanda matukinta ya yi

- Jirgin ya juyo lokacin da matukin jirgin ya lura da hasken wutan da ya bayyana sannan domin tsaro sai ya dawo filin jirgin na Lagas, wanda dama daga chan ya tashi

Wani jirgin kamfanin Arik Air, kirar Boeing 737-700 NG mai shawagi a W3 740 daga Lagas zuwa Port Harcourt a jiya Laraba, 25 ga watan Disamba ta yi dawowar gaggawa zuwa Lagas bayan matukin jirgin ya gano wani alama da ke nuna akwai matsala.

Jirgin ya juyo lokacin da matukin jirgin ya lura da hasken wutan da ya bayyana sannan domin tsaro sai ya dawo filin jirgin na Lagas, wanda dama daga chan ya tashi.

A wani jawabi, manajan sadarwa na kamfanin jirgin, Mista Banji Ola ya ce: “matukin jirgin ya kira sashin kula da cunkoson ababen hawa na sama wato Air Traffic Controller (ATC) on sanar masu da shawararsa da kuma kunna alamar neman agajin gaggawa. Hakan ya yi daidai da tsarin aiki kuma shine ya fi dacewa saboda tsaro.”

"Sannan sai aka samarwa fasinjojin na Port Harcourt wani jirgin domin cigaba a tafiyarsu, yayinda tawagar injiniyoyinmu ke aiki kan jirgin wanda ya koma mazauninsa.

KU KARANTA KUMA: Na taba siyar da biredi don haka ba zan iya koran masu kasuwanci a titi ba – Gwamna Makinde

“Don haka kamfanin jigin Arik Air na ba kwastamominta tabbacin cewa ba za ta taba wasa da tsaron da aka san jirgin dashi ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel