Na taba siyar da biredi don haka ba zan iya koran masu kasuwanci a titi ba – Gwamna Makinde

Na taba siyar da biredi don haka ba zan iya koran masu kasuwanci a titi ba – Gwamna Makinde

- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayyana dalilin da yasa bai kori masu talla a titunan jihar ba

- Makinde ya bayyana cewa shima ya taba tallan biredi a bakin hanya don haka ya san lamaran da ke tattare da hakan

- Ya ce har sai ya samar wa masu talla wajen zama kafin ya iya fatattakansu daga titi

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya bayyana dalilin da yasa bai kori masu talla a titunan jihar ba.

Gwamnan wanda kotun koli ta tabbatar da nasararsa a zaben watan Maris 2019 kwanakin baya ya ce, dalilin nasa ya kasance saboda halin rayuwar da ya tsinci kansa a lokacin da ya kasance dan talla a Yemetu, wani yanki da ke makwabtaka da Ibadan.

Gwamnan ya bayyana haka a babban masallacin Oja Oba, Ibadan, a lokacin wani addu’a na musamman domin tunawa da cikarsa shekara 52 a duniya.

Ya ce: “Wani ya bayyana cewa an aalakanta ni da fadin cewa ba zan kori masu kasuwanci a titi ba batare da nema masu mafita ba. Kwarai hakan gaskiya ne saboda na san abunda ke tattare da siyar da abu a titi. Na taba siyar da biredi a bakin hanyar Yemetu.

“Na fadi haka ne saboda ba zan iya koransu ba har sai mun samar masu da madadin nan. Kuma mun fara aiki kan haka. Mun yi hakan a Ojoo inda muka bukaci mutane da kada su yi kasuwanci a wajen da muke son gina tashoshin zamani.

KU KARANTA KUMA: Gaskiyar dalilin da ya sa ba mu saki Zakzaky tare da su Dasuki ba – Gwamnatin tarayya

Makinde ya gode ma mutanen kan addu’o’i da fatan alkhairi da suke masa.

Ya ce: “Addu’o’inku na da muhimmanci matuka a gare ni.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel