Gaskiyar dalilin da ya sa ba mu saki Zakzaky tare da su Dasuki ba – Gwamnatin tarayya

Gaskiyar dalilin da ya sa ba mu saki Zakzaky tare da su Dasuki ba – Gwamnatin tarayya

Ministan Shari'an Najeriya, Abubakar Malami ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ba ta saki Shugaban shi'a, Ibrahim El-Zakzaky tare da su Sambo Dasuki da Omowole Sowere bane saboda ba ta da hurumi na yiwa wata shari'a da ke hannun gwamnatin jiha katsalandan.

Furucin Malami na zuwa ne a daidai lokacin da mutane ke yamutsa gashin baki kan neman sanin lokacin a gwamnati za ta saki Shugaban na kungiyar IMN, biyo bayan sakin Dasuki da Sowere.

A ranar Talata, 24 ga watan Disamba ne gwamnatin ta bai wa hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) umarnin sakin mutanen biyu, sai dai ban da El-Zakzaky da shi ma ya dade a hannun hukumomin.

Malami ya kara da cewa: "Saboda haka gwamnatin tarayya ba za ta yi katsalandan a kan shari'a wadda hakkin bibiyarta yake na jiha ba nata ba."

Gwamnatin tarayya ta sha bayyana cewa ba ita ce ke rike da El-Zakzaky ba, gwamnatin jihar Kaduna ce ke tuhumarsa a gaban kotu.

KU KARANTA KUMA: Ina fatan tarihi zai yi min adalci - Buhari

A wani labari makamancin haka, mun ji cewa tsohon mai bada shawara a fannin tsaro, Sambo Dasuki ya yi bayani a kan garkamesa da gwamnatin tarayya tayi na shekaru hudu. Ya kara da bayyana cewa bashi da wata kulalliya tsakaninsa da kowa.

Dasuki ya bayyana cewa, wannan abun daga Allah ne ba daga kowa. Ya ce babu komai tsakaninsa da shugaba Muhammadu Buhari.

A wata tattaunawar da Dasuki yayi da muryar Amurka, ya yi bayanin cewa ya dena zuwa kotu ne saboda gwamnatin tarayya ta ki sakinsa duk da ya cika dukkan sharuddan belinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel