Ina fatan tarihi zai yi min adalci - Buhari

Ina fatan tarihi zai yi min adalci - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yana taka-tsan-tsan da aikinsa a matsayin Shugaban kasa. Ya ce tunda an rantsar dashi domin ya riki mulkinsa daidai da kundin tsarin mulkin Najeriya “sannan da izinin Allah,” zai bi tsarin yadda ya kamata har zuwa karshen wa’adin shugabancinsa.

Shugaban kasar ya kara da cewa yana fatan “fatan tarihi zai yi min adalci da yan Najeriya.”

Ya yi magana ne a jiya Laraba, 25 ga watan Disamba a fadar Shugaban kasa Abuja, lokacin da ya karbi bakuncin mazauna Abuja karkashin jagorancin ministan Abuja, Mohammed Bello, a lokacin ziyarar Kirisimeti.

Tawagar sun hada da shugabannin gargajiya, na addini da kuma na siyasa tare da ma’aikatan gwamnati a kuma manema labarai.

Buhari ya jadadda jajircewar gwamnatinsa na yin iya bakin kokarinta domin amfani da albarkatunta wajen sake gina kasar.

Ya tuna cewa ayyukan mayaka a Niger Delta ne ya kara tabarbarar da rashin ababen more rayuwa da gwamnatinsa ta gada.

KU KARANTA KUMA: Masu juya akalar mulki abun girmama wa ne, sun cancanci mutuntawa - Garba Shehu

Sai dai kuma ya nuna karfin gwiwar cewar a shekaru hudu da suka gabata, gwamnatin tarayya ta samu cigaba sosai wajen hada albarkatun kasa don sake gina ababen more rayuwa a fadin kasar.

Buhari ya bayyana shekarar 2019 a matsayin mai tarin nasara ga kasar, inda ya yi godiya ga yan Najeriya a kan imani da suka yi dashi da kuma mara ma gwamnatinsa baya wajen kai Najeriya zuwa mataki na gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel