Khadimul Islama: Gwamnatin Kano ta haramtawa mabanbantan jinsi hawa adaidaita sahu daya

Khadimul Islama: Gwamnatin Kano ta haramtawa mabanbantan jinsi hawa adaidaita sahu daya

- Gwamnatin jihar Kano ta haramtawa mutane mabanbantan jinsi hawa adaidaita sahu daya

- Kamar yadda Harun Ibn-Sina ya bayyana, gwamnatin jihar ta shirya tsaf don jaddada hukuncin addinin Islama

- A daidaita sahu ta fara zuwa Kano ne tun zamanin mulkin Shekarau bayan da ya haramtawa mata hawa achaba a fadin jihar

Gwamnatin jihar Kano ta haramtawa mutane mabanbantan jinsi hawa adaidaita sahu daya a fadin jihar daga watan Janairu 2020.

Gwamna Abdullahi Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin rufe bikin IVC da aka yi karo na 77 wanda kungiyar musulmai ta kasa ta shirya. Hakan ya faru ne jami'ar Bayero dake Kano.

Gwamna Ganduje wanda ya samu wakilcin shugaban hukumar Hisbah, Harun Ibn-Sina, ya ce gwamnatin jihar ta shirya tsaf wajen jaddada hukunce-hukunce addinin Islama.

DUBA WANNAN: Dasuki ya yi magana a kan cafkesa, ya bayyana abinda ke tsakaninsa da Buhari

Kamar yadda aka sani, an fara gabatar da adaidaita sahu ne a jihar Kano tun zamanin mulki Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a matsayin sufuri ga mata zalla.

Wannan ya biyo bayan haramta achaba daga daukar mata da tsohon gwamnan yayi.

Tun bayan saukar Malam Shekarau, adaidaita sahu sun koma daukar kowanne jinsi, lamarin da gwamnatin yanzu ta ce ba zata lamunta ba.

Hakazalika, Gwamna Ganduje ya yi kira ga daliban da su fuskanci karatunsu tare da watsi da ta'ammali da miyagun kwayoyi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel