Masu juya akalar mulki abun girmama wa ne, sun cancanci mutuntawa - Garba Shehu

Masu juya akalar mulki abun girmama wa ne, sun cancanci mutuntawa - Garba Shehu

Babban mai ba Shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Mallam Garba Shehu, ya karyata ikirarin cewa na kewaye da Shugaban kasa da ake yiwa lakabi da cabalsa sun kasance mutane masu iko da ke juya Shugaban kasa, Muhammadu Buhari wajen yanke manyan hukunci.

Shehu, wanda ya bayyana a matsayin bako a shirin Channels TV na Politics Today a ranar Laraba, 25 ga watan Disamba ya ce sabanin yadda mutane suka yarda cewa na kewaye da Shugaban kasar na juya shi, sun kasance yan Najeriya masu mutunci wadanda suka cancanci a mutuntasu saboda sun cimma nasarori da dama.

Hadimin Shugaban kasar wanda ya zargi yan Najeriya da juya magana ya tuna cewa mutane sun yarda cea majalisar tsohon Shugaban kasa Umaru Yar’aua a Goodluck Jonathan na cike da miyagu.

Shehu wanda ya bayyana cewa gata ne na musamman samun shiga majalisar Shugaban kasar ya ce idan ba don yarda ba da Shugaban kasar bai zabi mutum ba.

Ya kuma gargadi yan Najeriya da kada su lakaba wa mutane sunan miyagu don kawai saboda an basu damar yiwa kasa hidima ta hanyar samun kusanci da Shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Murnar zagayowar ranar haihuwa: Ban taba ganin dan siyasan daya kai Ganduje lissafi ba – Buhari

Furucin nasa na zuwa ne kasa da mako daya bayan an rahoto ina yace babu aibu don shugaba Buhari ya mallaki miyagu wajen tafiyar da gwamnati a yau a kullun.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel