Yansanda sun yi ram da barayin shanu 7, sun kwace dimbin makamai a Kano

Yansanda sun yi ram da barayin shanu 7, sun kwace dimbin makamai a Kano

Rundunar Yansandan jahar Kano ta sanar da samun nasarar cafke wasu kasurguman barayin shanu tare da kama dimbin makamai, kamar yadda kwamishinan Yansandan jahar, Habu Ahmed Sani ya tabbatar.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito kwamishinan Yansandan ya bayyana cewa barayin sun addabi yankunan jahohin Kaduna, Katsina da kuma jahar Kano, inda suke bi ruga rugan dabbobi suna kwashe shanun mutane.

KU KARANTA: Kodai ku tuba ku mika wuya, ko kuma karshenku ya zo kenan – Buhari ga miyagun Najeriya

“Barayin dabbobi 7 muka kama muka kama a Kano, Katsina da Kaduna ta hanyar amfani da na’urorin zamani. Mun kama bindigu kirar AK-47 guda hudu, bindigar toka, kakin Soji guda biyu da shanu 500.

“Barayin na da hannu cikin satar wasu kananan yara 10 da aka sacesu daga Kano zuwa garin Onitsha na jahar Anambra, haka zalika mun kwace babura biyu, motoci biyar, wukake 180, adduna 25, gorori 128 da kuma tarin ganyen tabar wiwi.” Inji shi.

Kwamishinan Yansanda ya kara da cewa sun kama wasu miyagun mutane biyu; Aminu Suleiman da Abdulrashid Ishaq dake unguwar Tudun Murtala da laifin satar wani yaro dan shekara 11 Ali Mohammed, inda suka kashe shi suka binneshi a unguwar Wase, cikin karamar hukumar Minjibir.

A wani labari kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gogaggen dan siyasa, kuma kwararre wanda ke yi ma jam’iyya bauta.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya sanar da haka a daren Laraba, 25 ga watan Disamba a babban birnin tarayya Abuja, inda yace: “Ganduje kwararren dan siyasa ne daya taimaka wajen gina jam’iyyar APC, tare da aiki tukuru wajen samun nasarar jami’yyar.

“Gwamnan Kano na daga cikin yan siyasa masu hakuri kuma masu lissafi da na taba gani a rayuwata, don haka Ganduje na da duk dalilan godiya ga Allah bisa kaiwa shekaru 70 a duniya cikin koshin lafiya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel