Kodai ku tuba ku mika wuya, ko kuma karshenku ya zo kenan – Buhari ga miyagun Najeriya

Kodai ku tuba ku mika wuya, ko kuma karshenku ya zo kenan – Buhari ga miyagun Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira da babban murya ga mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram, yan bindiga, yan fashi, masu garkuwa da mutane da masu cin dunduniyar tattalin arzikin kasa dasu tuba su mika wuya.

Buhari ya yi wannan kira ne yayin da gabatar da jawabin taya mabiya addinin Kirista murnar zagayowar ranar bikin Kirismeti a ranar Laraba, 25 ga watan Disamba, inda yace yana kira ga miyagun dasu daina abinda suke yi, su rungumi zaman lafiya kamar sauran yan Najeriya.

KU KARANTA: Da sauran rina a kaba: DSS ta kwace wayoyin salular Sowore bayan ta sake shi

“Idan kuma basu ji kiran da muke musu ba, tabbas karshensu ya zo kenan, saboda zaratan dakarun Sojinmu da sauran hukumomin tsaron Najeriya sun shirya tsaf domin fuskantarsu tare da karyasu.” Inji shi.

Haka zalika shugaba Buhari ya yi kira ga yan Najeriya su guji aikata duk wani mummunan aiki da ya saba ma bikin kirismeti, saboda a cewarsa dole ne sai jama’a sun nuna sadaukarwa sosai wajen zaman lafiya da lumana da makwabtansu ba tare da la’akari da bambance bambancen dake tsakaninsu ba.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gogaggen dan siyasa, kuma kwararre wanda ke yi ma jam’iyya bauta.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya sanar da haka a daren Laraba, 25 ga watan Disamba a babban birnin tarayya Abuja, inda yace: “Ganduje kwararren dan siyasa ne daya taimaka wajen gina jam’iyyar APC, tare da aiki tukuru wajen samun nasarar jami’yyar.

“Gwamnan Kano na daga cikin yan siyasa masu hakuri kuma masu lissafi da na taba gani a rayuwata, don haka Ganduje na da duk dalilan godiya ga Allah bisa kaiwa shekaru 70 a duniya cikin koshin lafiya.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Newspaper

Online view pixel