Murnar zagayowar ranar haihuwa: Ban taba ganin dan siyasan daya kai Ganduje lissafi ba – Buhari

Murnar zagayowar ranar haihuwa: Ban taba ganin dan siyasan daya kai Ganduje lissafi ba – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje a matsayin gogaggen dan siyasa, kuma kwararre wanda ke yi ma jam’iyya bauta.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ne ya sanar da haka a daren Laraba, 25 ga watan Disamba a babban birnin tarayya Abuja, inda yace: “Ganduje kwararren dan siyasa ne daya taimaka wajen gina jam’iyyar APC, tare da aiki tukuru wajen samun nasarar jami’yyar.

KU KARANTA: Da sauran rina a kaba: DSS ta kwace wayoyin salular Sowore bayan ta sake shi

“Gwamnan Kano na daga cikin yan siyasa masu hakuri kuma masu lissafi da na taba gani a rayuwata, don haka Ganduje na da duk dalilan godiya ga Allah bisa kaiwa shekaru 70 a duniya cikin koshin lafiya.” Inji shi.

Haka zalika shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Ganduje murnar lashe kambun gwarzon gwamnan jam’iyyar APC na shekarar 2019, kamar yadda kungiyar gwamnonin APC ta bayyana.

Gwamnonin na APC sun bayyana Ganduje a matsayin gwarzon gwamnan jam’iyyar daya ciri tuta wajen kirkirar manyan ayyukan more rayuwa tare da aiwatar dasu a jaharsa domin amfanin miliyoyin al’ummar Kanawa.

Mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwar ne ya bayyana zarran da Ganduje ya yi yayin ganawa da manema labaru a jahar Kano a ranar Laraba, inda yace watanni uku a jere (Satumba, Okotoba da Nuwamba) Ganduje ke kan gaba wajen ayyuka a tsakanin gwamnonin APC.

Sauran jahohin dake bin jahar Kano sun hada da Yobe, Borno, Edo, Gombe, Kaduna, Legas, Ogun, Nassarawa, Katsina, Kebbi, Kwara, Osun, Neja, Ondo, Kogi da kuma Filato.

A wani labarin kuma, shugaba Buhari ya yi kira da babban murya ga mayakan kungiyar ta’addanci na Boko Haram, yan bindiga, yan fashi, masu garkuwa da mutane da masu cin dunduniyar tattalin arzikin kasa dasu tuba su mika wuya.

Buhari ya yi wannan kira ne yayin da gabatar da jawabin taya mabiya addinin Kirista murnar zagayowar ranar bikin Kirismeti a ranar Laraba, 25 ga watan Disamba, inda yace yana kira ga miyagun dasu daina abinda suke yi, su rungumi zaman lafiya kamar sauran yan Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel