Ganduje ya sake zama gwarzon gwamnonin APC

Ganduje ya sake zama gwarzon gwamnonin APC

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kara bayyana a matsayin gwarzon gwamnoni kamar yadda binciken kungiyar gwamnonin APC ta bayyana a fannin aiyukan ci gaba a jihohin APC.

A yayin zantawa da manema labarai a ofishinsa a ranar Laraba, babban sakataren yada labarai na gwamnan, Malam Abba Anwar ya ce wannan binciken na kungiyar gwamnonin hanya ce ta assasa mulki nagari tsakanin gwamnonin APC a Najeriya.

Ya yi bayanin cewa, “a karkashin wannan salon ne ake duba aiyukan gwamnonin APC a duk wata. Ana duba kusan duk bangarori na gwamnati da suka hada da Lafiya, ilimi, noma da kiwo, gidaje, sufuri, tsaftace muhalli da sauransu. Dukkan sauran jihohin ana duba su tare da tantancewa.”

DUBA WANNAN: Tsaro: Jerin sunayen sabbin AIG da kwamishinonin da IGP ya nada

Kamar yadda ya ce, “a cikin watanni uku a jere, Ganduje ne ke kan gaba daga watan Satumba, Oktoba zuwa Nuwamba na shekarar nan. Kano ce a gaba wajen samun cigaba daga mataki zuwa mataki.”

Ya kara da cewa, “A wata wasika mai kwanan wata 7 ga watan Oktoba, 2019, kuma darakta janar na wannan kungiyar, Salihu Mohammed Lukman yasa hannu, an bayyana jihar Kano a kan gaba ta bangaren kiwon lafiya, ilimi, tsaro, sufuri, walwala, wutar lantarki, shari’a da wayar da kai.

"A haka ne ta samu maki 18. Jihar Yobe ce ke biye da ita da maki 14, Borno da maki 13, jihohin Edo, Gombe, Kaduna, Legas , Ekiti da Ogun sun samu maki 12 kowannensu. Jihar Nassarawa na da maki 9, Katsina da Kebbi na da 7 kowannensu, Kwara da Osun na da 6 kowannensu, Niger na biye da maki 5, Ondo na da 4 sai karshe Kogi da Filato ke da uku-uku.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel