Wike ya tona asirin wani gwamnan PDP da ke shirin komawa APC

Wike ya tona asirin wani gwamnan PDP da ke shirin komawa APC

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya zargi Gwamnan jihar Bayelsa mai sauka, Seriake Dickson da shirye-shiryen komawa jam'iyyar APC don gujewa yuwuwar cafkesa daga hukumar yaki da rashawa ta EFCC, bayan wa'adin mulkinsa ya kare.

Idan zamu tuna, Wike da Dickson sunyi hannun rigane tun bayan da jam'iyyar PDP ta sha mugun kaye a zaben jihar Bayelsa da ya gabata.

A takardar da mataimakin Wike a fannin yada labarai, Simeon Nwakaudu ya fitar, ya ce "Dickson ya kammala shirye-shiryen komawa APC tare da tunanin hukumar yaki da rashawa ta EFCC ba zata cafkesa ba in ya bar gwamnati."

DUBA WANNAN: Jigo a APC ya yabawa Buhari kan nasarorin da ya samu a zabe, tattalin arziki da tsaro

Ya zargi Dickson da tozartawa da cin amanar mutanensa ta hanyar kin amfani da albarkatun jihar yadda ya dace.

Ya ce ,"a matsayin Bayelsa na karamin gari, ba dai-dai bane a ce gwamnan ya banzatar da kudi har naira biliyan 70 a kan filin saukar jirgin saman da ba a kammala ba. Duk da kuwa jihar Bayelsa na bukatar tituna da manyan abubuwan more rayuwa."

Wike ya bayyana cewa, ya yi wa jihar Ribas kokari a cikin shekaru hudu fiye da yadda Dickson ya yi wa Bayelsa a cikin shekaru takwas.

Ya kara da jan kunnen Dickson da ya guji yada labaran karya da farfaganda game da shi da kuma mulkinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel