Sule Lamido Ramuwar gayya ce ta sa Shugaba Buhari ya garkame Dasuki ba sata ba

Sule Lamido Ramuwar gayya ce ta sa Shugaba Buhari ya garkame Dasuki ba sata ba

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce sakin Sambo Dasuki da Ministan shari’a ya sa aka yi, ya nuna cewa tun farko ba zargin satar kudi ta sa aka kama shi ba.

The Guardian ta rahoto Alhaji Sule Lamido ya na cewa garkame tsohon Mai bada shawara a kan harkar tsaron bai da wata alaka da badakalar kudin makamai na Dala biliyan 2.1.

‘Dan siyasar ya fadawa ‘Yan jarida a wayar tarho cewa tsare Sambo Dasuki da aka yi, ya na da nasaba ne da sabanin da ke tsakaninsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“Babu abin da ya hada (kama shi da aka yi) da rashin gaskiya. An gayyaci Dasuki an yi masa tambayoyi wanda bayan nan aka gurfanar da shi a gaban kuliya da zargin laifi."

“Cigaba da tsare shi na kwana guda bayan kotu ta bada belinsa ya sabawa doka, bai dace ba, kuma bai kamata gwamnati ta yi wannnan aikin duhun kai ba. Ba batun kudi bane.”

KU KARANTA: Dasuki ya musanya zargin wata rigima tsakaninsa da Buhari

Akwai hukuncin da Alkali mai shari’a Binta Nyako, ta yi na cewa bai halatta a kama mutum a rufe a kan umarnin wani babban jami’in gwamnati ba, har ma shugaban kasa.

“Bai yi laifin komai ba, idan ana maganar rashin gaskiya ko bacewar kudi. (Dasuki) ya bi umarnin da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya ba shi ne." Inji Sule Lamido.

Tsohon Ministan wajen ya ce: “Surutun Mutane ya sa gwamnati ta yi abin da ya dace. Dama can Buhari ya na da tarihin sabawa doka. Daure Dasuki kadan daga cikin aikin sa ne.”

Sule Lamido ya nuna cewa Najeriya ta shiga matsala a irin wannan mulki mai-ci, ganin yadda Buhari ya taba fitowa karara ya ce ya raina tsarin tafiyar mulkin fafar hula.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Online view pixel