Lawan da Okowa sun yi tir da harin da aka kai a gidan Goodluck Jonathan

Lawan da Okowa sun yi tir da harin da aka kai a gidan Goodluck Jonathan

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawan, ya soki harin da wasu Miyagu su ka kai har gidan tsohon shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan.

Kamar yadda mu ka ji, Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ya bayyana wannan hari a Kauyen tsohon shugaban na Najeriya a matsayin abin Allah-wadai.

Sanatan ya yi wannan jawabi ne ta bakin wani daga cikin Hadimansa, Ola Awoniyi a jiya Ranar Talata 24 ga Watan Disamba, 2019, a Garin Abuja.

Ahmad Lawan ta bakin Ola Awoniyi ya ke cewa wannan hari da aka kai a gidan tsohon shugaban Najeriyar ya cika dabbanci da karshen ta’addanci.

A cewar shugaban majalisar dattawan kasar: “Ya kamata kowane mai hankali a Najeriya ya soki wannan hari da aka kai ba tare da wata-wata ba.”

KU KARANTA: Buhari ya kira Jonathan bayan abin da ya auku da shi a gidansa

Lawan da Okowa sun yi tir da harin da aka kai a gidan Goodluck Jonathan

Ahmad Lawan ya soki Miyagun da su ka kai hari a gidan Goodluck Jonathan
Source: Twitter

Lawan a jawabin na sa ya ke cewa harin ya sabawa tunani na hankali, inda ya kara da kira ga hukuma ta gudanar da bincike na musamman.

Sanata Lawan ya bukaci jami’an tsaro su gudanar da bincike domin a iya hukunta wadanda su ka yi wa shugaban wannan mummunan ta’adi har gida.

Har ila yau, Ahmad Lawan ya jinjinawa kokarin Jami’an tsaron da ke bakin aiki a gidan tsohon shugaban kasar lokacin da aka kai harin a jiya.

Lawan ya kuma yi ta’ziyya ga Iyalin jami’in da ya rasa ransa. Shi ma gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya bi sahu, ya soki wannan mugun hari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel