Dalilin da yasa har yanzu Buhari bai canja shugabanin tsaro ba - Sanata Ali Ndume

Dalilin da yasa har yanzu Buhari bai canja shugabanin tsaro ba - Sanata Ali Ndume

- Sanata Ali Ndume ya ce shugaban kasa Buhari ba zai iya nada sabbin shuwagabannin tsaro ba a yanzu

- Dan majalisar ya ce a yanzu Najeriya na zamanin yaki ne kuma ba zata iya samun sabbin shuwagabannin tsaro ba

-Ndume ya bayyana cewa, da sauya wajen aiki na sojin, akwai yuwuwar a shawo kan matsalar tsaro da ta yi katutu a kasar nan

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, Sanata Ali Ndume, ya bada dalilin da suka sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai iya sauya shuwagabannin tsaro ba a Najeriya.

Ndume, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattijai a kan al’amarin sojin kasar nan, ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin tattaunawa da manema labarai. An tambayesa dalilin da yasa Shugaba Buhari bai sauya shuwagabannin tsaro ba. Ya bayyana cewa, a halin yanzu Najeriya na zamani ne na yaki.

Dan majalisar ya ce, Shugaba Buhari bashi da wani zabin da ya wuce rike shuwagabannin tsaron, ba saboda halin da yankin Arewa maso gabas ke ciki ba kadai, har da dukkan Najeriya.

DUBA WANNAN: Kano: Sanusi ya haramta wa 'Sokon' Kano shiga fada har abada

Ya ce, da sauyin wajen aiki mai karfi, Najeriya zata iya shawo kan matsalar tsaro a jihohi daban-daban na kasar nan kuma zaman lafiya zai tabbata.

Ndume y ace: “Muna cikin yaki ne. Yaki babba kuwa. Muna yakar ta’addanci a Arewa maso gaba da kuwa arewa maso yamma.”

Dan majalisar ya ce, Sojin Najeriya sun mayar da hankali ba kadan ba wajen shawo kan matsalar rashin tsaro na kasar nan.

Ndume ya kara da bayyana cewa, zai yi aiki da mataimakin shugaban majalisar dattijai Omo Ovie-Agege don tabbatar da ‘yan Najeriya sun samu irin aiyukan da suka kamata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel