Asiri ya tonu: An kama mutane 4 sanye da kayan sojoji suna kokarin fashi a banki

Asiri ya tonu: An kama mutane 4 sanye da kayan sojoji suna kokarin fashi a banki

- Wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sanye da kayan sojoji, sun shiga hannun ‘yan sanda

- Rundunar ‘yan sandan ta bibiyesu ne bayan bayanin sirrin da ta samu na cewa zasu yi wa wani banki fashi a jihar Ekiti

- Shugaban kungiyar sojojin bogin ya bayyana cewa, sun samu hadin kan daya daga cikin manajojin bankin tare da ma’aikata 6 na bankin

Wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan fashi ne da kayan sojoji sun shiga hannun jami’an tsaro bayan da suka yi yunkurin fashi da makami a wani banki. Jami’an ‘yan sandan Ibadan, jihar Oyo a karkashin shugabancin IGP ne suka cafke wadanda ake zargin.

Wadanda ake zargin sune: Matthew Olagoke, Ahmed Abdulahi, Johnson Ojo da Adebanjo Bamidele, wadanda ke shirin harar bankin a jihar Ekiti a ranar 7 ga watan Dismaba. Jami’ai na musamman karkashin rundunar ‘yan sandan jihar sun gano shirinsu inda suka bibiyesu har Ibadan yayin da suke hanyarsu ta zuwa Ekiti suka cafkesu.

Kwamishina Kenneth Ebrimson, wanda ya kamo wadanda aka zargin ya bayyanawa manema labarai cewa, ‘sojojin bogi’ ne mutanen. An kamasu da bindigogi uku, harsasai 20, katin shaida uku, ATM uku, wayoyi 7 da laya.

Jaridar The Nation ta gano cewa, babban mashiryin harin shine wani kofur din soja mai suna Adebamji Bamgboye wanda aka kora daga rundunar sojin.

KU KARANTA: Labari mai dadi: Za'a fara kera wasu bangarori na jikin jirgin sama a Najeriya

An cafke wadanda ake zargin ne a sabuwar kasuwar Gbagi dake kan babban titin Ibadan zuwa Ife a Ibadan.

Ebrimson ya ce, kungiyar sun kware wajen fashi a gidan mai, bankuna tare da dakunan kwanan dalibai na cikin manyan makarantun kasar nan. Ya kara da cewa, sun hari jami’ar Ibadan da jami’ar kimiyya ta tarayya da ke Akure.

A yayin zantawa da manema labarai, shugaban kungiyar sojojin bogin, Bamgboye ya ce yana jagorantar su ne don su yi fashi da makami ga bankin bayan sun samu hadin kan wani manajan inshora tare da ma’aikata 6 na bankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel