Jigo a APC ya yabawa Buhari kan nasarorin da ya samu a zabe, tattalin arziki da tsaro

Jigo a APC ya yabawa Buhari kan nasarorin da ya samu a zabe, tattalin arziki da tsaro

- Jigo a jam'iyyar APC, Waziru Bulama ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari kan nasarorin da ya samu a fanin tsaro, tattalin arziki da zabe

- Mista Bulama ya ce nasarorin da gwamnatin Buhari ta samu ne yasa 'yan Najeriya suka sake zabensa a 2019

- Mista Bulama ya rike mukamamin mataimakin manajan yakin neman zaben shugaban kasa a zaben 2019

Jigo a jam'iyyar All progressives Congress, APC, Waziri Bulama, ya jinjinawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan gudanar da zaben cikin zaman lafiya, farfado da tattalin arziki da kuma magance batun rashin tsaro a kasar.

Mista Bulama wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin manajan yakin neman zaben shugaban kasa a zaben 2019, ya yi wannan jawabin ne yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Kano: Sanusi ya haramta wa 'Sokon' Kano shiga fada har abada

A cewarsa, sakamakon babban zaben 2019 da Buhari ya lashe ya nuna gaskiya cewa 'yan Najeriya sun gamsu da kamun ludayin gwamnatin na APC tun shekarae 2015.

Ya ce, "'Yan Najeriya sun gamsu da irin tsarin shugabancinsa da tsare-tsarensa. Wannan shine dalilin da yasa aka sake zaben shi karo na biyu da kuri'un da suka dara wanda ya samu a zaben 2015 a kuma wuraren da bai samu kuru'un ba ma a 2015.

"Akwai matsalar rashin tsaro da ta adabi Najeriya a 2014 da 2015 a lokacin da 'yan ta'addan kungiyar Boko Haram suka karbe iko a wasu sassan Najeriya.

"Tattalin arziki ya tsaya cak, kimanin jihohi 30 ba sa iya biyan albashi, har hukumomin gwamnatin tarayya ma da kyar suke iya biyan albashi, masu fansho suna wahalar samun hakokinsu.

"Amma kawo yanzu, mun warware matsalolin da yawa, mun samar da tsaro a Najeriya, mun kwato mafi yawan garurruwan da 'yan ta'adda ke cin karensu babu babbaka."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel