An kashe mayakan Boko Haram 48 a jajiberin Kirsimeti

An kashe mayakan Boko Haram 48 a jajiberin Kirsimeti

Sojin Najeriya tare da ‘yan sa kai sun yi nasarar fatattakar mayakan Boko Haram da suka kai hari Biu da ke Kudu da jihar Borno, in ji wani jami’i. Wani jami’in farar hula na JTF wadanda suke yakar ‘yan ta’addan tare da rundunar sojin, ya sanar da jaridar Premium Times yadda mayakan Boko Haram 48 suka mutu a yakin. Har yanzu dai ba a ji ta bakin rundunar sojin ba.

A ranar Talata ne jaridar Premium Times ta ruwaito yadda mayakan Boko Haram din suka taru a Biu don harar garin bayan kasa da sa’o’i 24 da sojin suka fatattakesu.

A ranar Litinin, mayakan sun hari Biu inda suka afkawa kauyuka uku tare da kashe mutane biyu da raunata 13. Daga bisani ne sojin suka fatattaki mayakan bayan musayar wuta da ta wakana a tsakaninsu.

A washegarin ranar Litinin din ne, kuma jajiberin Kirsimeti da misalin karfe 6 na yamma aka gano mayakan sun kara komawa Kimba gab da garin Biu na jihar Barno.

DUBA WANNAN: Kaico: Yadda Dasuki ya rasa jana'izar mahaifinsa

An gano cewa, rundunar sojin Biu tare da na Damboa suka hada kai inda suka yi musayar wuta tsakaninsu da mayakan. Wannan musayar wutar ta kaisu har karfe 4 na asuba.

Bayan nan ne sojojin suka duba gawawwaki inda suka gano sun halaka mayakan Boko Haram 48 tare da cafke wasu mutane uku daga ciki a raye.

Duk da rundunar sojin bata fitar da wata takarda dangane da hakan ba, ‘yan yankin sun tabbatar da cewa komai ya koma lafiya a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel