Kirsimeti: Dan majalisa musulmi ya bada buhunan shinkafa 1,100 da Shanu 24 ga mazabarsa

Kirsimeti: Dan majalisa musulmi ya bada buhunan shinkafa 1,100 da Shanu 24 ga mazabarsa

- Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Pankshin-Kanke-Kanam a jos ya gwangwaje 'yan mazabarsa da kyauta

- Ya bada buhunan shinkafa 1,100 tare da Shanu 24 don su yi bikin Kirsimeti cikin walwala da jin dadi

- Ya bukaci 'yan mazabar da su yi masa addu'a da sauran shuwagabanni da su mulkesu cikin salama

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Pankshin-Kanke-Kanam a tarayya, Yusuf Gagdi, ya gwangwaje mazabarsa da buhuna 1,100 na shinkafa da Shanu 24 don taya su murnar bikin Kirsimeti, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Gagdi wanda ya gabatar da kayayyakin a ranar Talata a Pankshin, ya ce wannan karamci ya yi shi ne don goyon bayan ‘yan mazabarsa, ballanta masu karamin karfi don su yi bikin cikin jin dadi.

Ya bayyana cewa, “Duk da ni Musulmi ne, na yadda cewa Kirsimeti lokaci ne na yada kauna da abubuwan rayuwa tare da wadanda basu da karfi. Ko kafin in zama wakilin jama’a, na kasance ina yin hakan.”

DUBA WANNAN: El-Zakzaky: Ayatollah Ramazani ya bukaci kasashen duniya su matsa wa Najeriya lamba

“A yau, ina raba buhunan shinkafa 1,100 da Shanu 24 ga kungiyoyi daban-daban na fadin kananan hukumomi uku da ke karkashina. Ba dole wannan ya isa ba amma ina tunanin zai tallafawa wasu iyalan wajen murnar bikin Kirsimeti,” in ji shi.

Gagdi ya yi kira ga jama’a da su yi amfani da wannan lokacin wajen addu’a garesa da sauran shuwagabannin da ke fadin kasar nan. Yana fatan su shugabanci mutane cikin zaman lafiya da wadatar arziki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel