Sowore da Dasuki: Falana ya nemi Gwamnatin Buhari ta saki su El-Zakzaky

Sowore da Dasuki: Falana ya nemi Gwamnatin Buhari ta saki su El-Zakzaky

Babban Lauyan Najeriya kuma fitaccen Mai kare hakkin Bil Adam, Femi Falana SAN, ya yi magana bayan gwamnatin tarayya ta saki Sambo Dasuki da Omoyele Sowore.

A wani jawabi da ya fitar a Ranar Talata, 24 ga Watan Disamban 2019, Lauyan ya tabbatar an saki Jagoran tafiyar #RevolutionNow, Yele Sowore, da kuma Kanal Sambo Dasuki.

“Tun da gwamnatin Muhammadu Buhari ta fara bin doka yanzu, Malami (Ministan shari’a) ya yi kokarin ganin an bi duk wasu tsayayyun umarni da kotu su ka bada a baya.

A game da wannan, fitaccen Lauyan ya bukaci a saki Jagoran kungiyar IMN ta Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky da Mai dakinsa wadanda aka kama tun 15 ga Watan Disamban 2015

KU KARANTA: Jagoran Shi'a ya na so a matsa lamba wajen ganin an saki El-Zakzaky

Kotu ta bada belin Zakzaky da Matarsa, Zeenat El-Zakzaky, amma har yanzu su na tsare. Falana ya kuma bukaci a fito da duk wani da aka garkame ba tare da bin ka’ida ba.

Femi Falana ya bayyana cewa tun farko jami’an DSS ba su sake kama Olawale Bakare a lokacin da su ka shigo cikin kotu su ka yi ram da Takwaransa Omoyele Sowore ba.

Falana ya tunawa gwamnati cewa kotu ta haramtawa gwamnati cigaba da tsare Zakzaky da Iyalinsa tun 2016 har ma an ci ta tara, kuma an umarci ta gina masu gida.

A jawabin, Lauyan ya bayyana cewa gwamnatin ta rusa kujerar da ta hau na cewa sha’anin tsaro ya na gaban ‘yancin ‘Dan Adam, wanda da shi ta fake aka tsare mutanen.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel