Sasanci ya gagara a PDP bayan Wike ya ce Dickson ya juyawa Jam’iyya baya

Sasanci ya gagara a PDP bayan Wike ya ce Dickson ya juyawa Jam’iyya baya

Rikicin gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike da Takwaransa na jihar Bayelsa, Seriake Dickson, ya dauki wani sabon salo a lokaci da Nyesom Wike ya ki amincewa da yunkurin sulhu.

Gwamna Nyesom Wike ya yi watsi da shirin da jam’iyyar PDP ta ke yi na sasanta rikicin da ya barke tsakaninsa da gwamnan Bayelsa a dalilin batun rijiyoyin man kasar da ke yankin.

Wike ya ke cewa babu dalilin jam’iyya ta shigo cikin maganar tun da Alkalin babban kotun tarayya da ke Garin Abuja ya yanke hukunci game da abin da ya jawo sabanin da aka samu.

Gwamnan ya ce: “Ban san abin da ya sa su ke shigowa cikin matsalar ba. Ba su da karfin ikon sasanta maganar rijiyoyin mai. Na biyu kuma kotu da ke da cikakken iko ya bada hukunci.”

KU KARANTA: Buhari ya yi magana game da rade-radin zai sake zarcewa har 2027

Sasanci ya gagara a PDP bayan Wike ya ce Dickson ya juyawa Jam’iyya baya

Yunkurin yi wa Gwamnonin PDP sasanci ya gamu da cikas a hannun Wike
Source: Facebook

“Duk wanda bai yarda da wannan shari’a ba, ya je ya daukaka kara. Su na kokarin yin sulhu a madadin wanda ya yaudari jam’yya. Sun san cewa Seriake Dickson ya saida PDP.”

“Sun san cewa a zaben 2019 a jihar Ribas, Dickson Abokan hamayya ya yi wa aiki. Mutane daga ko ina a fadin kasar nan su na kira su ji abin da ake ciki. Dickson bai taba kira ba.

Alakar da ya ke da ita da jam’iyyar adawa ta jawo haka. Ina da hujar da ke nuna cewa Dickson ya zabi ya yi wa APC aiki. Ba zan zauna da kowa a game da batun gwamna Dickson ba.

"Ban da wata alaka da shi gwamna Dickson. Kai kamata ya yi gwamna Dickson ya yi murabus daga jam’iyyar zuwa yanzu, saboda shugabannin PDP su sake tado jam’iyyar a Bayelsa."

"Ina jam’iyyar ta ke a lokacin da Dickson ya bada ita? Meya hana su magana a lokacin. Ba za a yi wannan da ni ba, kuma babu wanda zai hana ni." Wike ya fadi wannan Ranar Talata.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel