Kirsimetin 2019: Buhari ya saki tsoho mai shekaru 75 tare da wasu mutane 18 daga gidan gyaran hali

Kirsimetin 2019: Buhari ya saki tsoho mai shekaru 75 tare da wasu mutane 18 daga gidan gyaran hali

Wani kwamitin rage 'yan gidan gyaran hali da kuma gyara, masu aiki a madadin shugaban kasa Buhari ya saki mutane 19 da suka hada da wani tsoho mai shekaru 75 da dan shi.

An sako tsohon ne daga gidan gyaran hali dake Kuje, babban birnin tarayya na Abuja. Mutumin da dansa sun kwashe shekaru 13 a gidan gyaran halin yayin da suke jiran hukunci. Duk 'yan gidan yarin da aka saki ba a bayyana sunansu ba, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Shugaban kwamitin shugaban kasar kuma babban alkalin kotun babban birnin tarayyar, Jastis Ishaq Bello ya ce, an saki 'yan gidan gyaran halin ne saboda shekaru, rashin halin biyan tara, rashin lafiya da kuma dadewa a gidan. Sun kai ziyarar ne a ranar 19 ga watan Disamba.

DUBA WANNAN: El-Zakzaky: Ayatollah Ramazani ya bukaci kasashen duniya su matsa wa Najeriya lamba

Jastis Bello ya ce hakan na daga cikin hangen nesa na Shugaba Buharin wajen rage yawan mutanen da ke tsare. Hakan ya yi dai-dai da tanadin adalci da hakkin dan Adam na duniya. Ya ce kwamitin na kokari wajen ganin an inganta bangaren koyon sana'a ta wadanda aka sakin bayan sun kammala zaman gidan gyaran halin.

Bello ya yi kira ga babban alkalin majistare din da ya guji ajiye mutane a gidan gyaran halin su dade, ba tare da an kammala shari'arsu ba kuma an bayyana laifin duarin nasu.

Tun a lokacin da aka kirkiri kwamitin shugaban kasar, sun ziyarci gidajen gyaran hali 36 a jihohi 17 a cikin kasar nan. 'Yan gidan yari 3,813 ne aka saka a cikin wannan lokacin.

Gidan gyaran halin na Kuje an gina shi ne don daukar mutane 560, amma a halin yanzu akwai mutane 1010. A kalla 822 daga ciki ne suke jiran hukunci yayin da 145 an riga an yanke musu hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel