Kaico: Yadda Dasuki ya rasa jana'izar mahaifinsa

Kaico: Yadda Dasuki ya rasa jana'izar mahaifinsa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda mahaifin Sambo Dasuki ya rasu. Mahaifinsa shine tsohon Sarkin musulmi, Ibrahim Dasuki. Ya rasu ne a watan Nuwamba 2016 yayin da Sambo yake garkame.

Dasuki bai samu halartar jana'izar mahaifinsa ba saboda duk rokon da aka yi wa Shugaban kasa Buhari don ya samu jana'izar, ya tashi a tutar babu.

Sarkin musulmi Dasuki ya rasu ne a lokacin da yake da shekaru 93 a duniya. Bayan jinya a wani asibitin kasar Turkiyya da ke Abuja, ya rasa ransa.

A zamanin mulkin Janar Sani Abacha ne aka sauke sarkin musulmin na 18.

DUBA WANNAN: El-Zakzaky: Ayatollah Ramazani ya bukaci kasashen duniya su matsa wa Najeriya lamba

A jiya ne gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin sakin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro (NSA), Sambo Dasuki, da kuma jagoran yunkurin gudanar da zanga-zanga a kasa, Omoyele Sowore.

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma aministan shari'a, Abubakar Malami, shine ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar da shi ranar Talata.

Malami ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar bayar da umarnin sakinsu ne domin yin biyayya ga umarnin kotuna a kan bayar da belinsu.

"Muna kira garesu da su kasance masu biyayya ga sharudan da aka bayar da belinsu a kai, sannan su guji aikata duk wani abu da kan iya zama ya saba wa doka da tsaro domin za a cigaba da tuhumarsu a gaban kotu bisa dokokin kasa," a cewar Malami.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel