‘Yan Majalisar Amurka 6 su ka aikowa FG takarda a kan Sowore da Dasuki

‘Yan Majalisar Amurka 6 su ka aikowa FG takarda a kan Sowore da Dasuki

A jiya ne gwamnatin Najeriya ta fito da tsohon Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Sambo Dasuki, wanda ya yi shekaru hudu a tsare duk da kotu ta bada belinsa.

Haka zalika an saki Omoyele Sowore wanda ya ke ta faman shiga hannun jami’an hukumar DSS tun cikin Watan Agusta. A farkon watan nan ne kuma aka sake cafke shi a harabar kotu.

Wasu Jaridun Najeriya sun bi diddiki domin gano abin da ya sa gwamnatin shugaba Buhari ta hakura ta fito da wadannan fitattun mutane biyu da ta ke zarginsu da manyan laifuffuka.

Ana zargin cewa an ga wasu daga cikin jami’ar kasar Amurka da ke aiki da ofishin Jakadancin kasar da ke Najeriya a zaman kotun da aka yi domin sauraron shari’ar Omoyele Sowore.

A wata takarda da ta shigo hannunmu, mun fahimci cewa ‘Yan majalisar Wakilan Amurka 6 su ka aikowa Ministan shari’a wasika su na neman ya bi abin da doka ta ce, ya saki mutanen.

An turowa Minista Abubakar Malami wannan doguwar takarda ne a Ranar 20 ga Watan Disamba. Idan ba ku manta ba, kafin nan Ministan ya nemi DSS ta janye hannunta daga shari’ar.

KU KARANTA: Jami'an DSS sun fito da Sambo Dasuki bayan dogon tsari

‘Yan Majalisar Amurka 6 su ka aikowa FG takarda a kan Sowore da Dasuki

Amurka ta matsa lamba wajen ganin an bi doka a shari'ar Sowore
Source: Depositphotos

Robert Menendez, Charles Schumer, Christopher A.C, Cory Booker, Bill Pascrell da Josh Gottheimer su ne ‘Yan majalisar Amurkan da su ka aikowa Ministan shari’ar wasika a makon jiya.

Sake cafke Sowore da aka yi a cikin zauren kotu a Ranar 6 ga Watan Disamban 2019, ne ya jawowa gwamnatin Najeriya ce-ce-ku-ce da surutu har daga kasashen ketare irin Amurka.

Jami’an tsaro masu fararen kaya ne su ka mamaye harabar kotu, su ka yi ram da Sowore yayin da kotu ta kammala wata zama. An yi wannan ne jim kadan bayan an bada belinsa da kyar.

Shi kuwa Kanar Sambo Dasuki mai ritaya ya na garkame ne tun Ranar 1 ga Watan Disamban 2015. Ana zargin Sambo Dasuki da hannu a wata badakalar sayen makamai ta Dala biliyan 2.1

Alkalai da-dama sun bada umarni a saki tsohon NSA na kasar amma gwamnati ta kauda idanunta sai yanzu. Wasu su na ganin cewa gwamnatin shugaba Buhari ta riga ta yi barna.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel