Sakin Dasuki da Sowore: Mutane hudu da suka shawo kan Buhari

Sakin Dasuki da Sowore: Mutane hudu da suka shawo kan Buhari

- Tsohon ministan sufurin jirgin sama kuma jigo a jam'iyyar PDP ya bayyana wadanda suka shawo kan Buhari har aka saki Dasuki da Sowore

- Kamar yadda Femi Fani-Kayode yace, Abba Kyari, Hadi Sirika, Malami da Kayode Fayemi suka taka rawar gani

- Ya bayyanasu a matsayin masu fadi a ji a gwamnatin Buhari kuma sun cancanci jinjina

Tsohon ministan sufurin jiragen sama kuma jigo a jam’iyyar PDP, Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa Abba Kyari, Malami, Hadi Sirika da Kayode Fayemi ne suka shawo kan Buhari har ya amince da sakin Sambo Dasuki da Omoyele Sowore.

Ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami a ranar Talata ya umarci jami’an tsaron farin kaya da su saki Sambo Dasuki da Sowore wadanda aka bada belinsu tuntuni.

DUBA WANNAN: El-Zakzaky: Ayatollah Ramazani ya bukaci kasashen duniya su matsa wa Najeriya lamba

An garkame Dasuki ne tun a watan Yuni na 2015 yayin da Sowore na garkame ne tun a ranar 3 ga watan Agusta.

A yayin zantawa kan yadda aka sakesu, Femi Fani-Kayode a ranar Talata ya wallafa a shafinsa na tuwita, ya ce: “Da kwarin guiwa zan iya cewa mutane hudu ne suka tsaya tsayin daka har aka saki Dasuki da Sowore. Sune suka shawo kan shugaban kasa Muhammadu Buhari har ya bada umarnin sakinsu. Abba Kyari, Malami, Hadi Sirika da Kayode Fayemi ne. Sune jigo kuma masu fadi a ji a gwamnatin Buhari. Ina jinjina musu.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel