Jajiberin Kirsimeti: Osinbajo ya ziyarci Buhari, ya bashi kyauta ta musamman

Jajiberin Kirsimeti: Osinbajo ya ziyarci Buhari, ya bashi kyauta ta musamman

A yayin da aka shiga jajiberin bikin Kirsimeti, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

A sakon da mai taimaka wa shugaban kasa a bangaren kafafen sadarwa na zamani, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Tuwita, ya ce Osinbajo ya ziyarci ofishin Buhari ne domin gabatar da kyautar katin taya shi murnar ganin karshen shekarar 2019.

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranar Laraba, 25 ga wata, da ranar Alhamis, 26 ga watan Disamba 2019, da kuma ranar Laraba, 1 ga watan Janairu, 2020, a matsayin ranakun hutun bikin Kirsimeti da kuma sabuwar shekara.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya sanar da hakan a cikin sanarwa da sakataren ma'aikatar harkokin cikin gida, Barista Georgina Ehuriah, ya fitar ranar Alhamis, 19 ga watan Disamba.

Da yake taya 'yan Najeriya da ke zaune a gida da ketare murnar zagayowar lokacin bikin Kirsimeti na wannan shekarar, Aregbesola ya bukaci mabiya addinin Kirista da su kasance masu koyi da biyayya ga koyarwar Yesu Almasihu a kan kaunar juna da zaman lafiya.

Kafin fitowar wannan sanarwa, Legit.ng ta wallafa rahoton cewa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya jagoranci zaman majalisar zartar wa ta tarayya (NEC) na ranar Alhamis a fadar shugaban kasa, Villa, dake Abuja.

Jajiberin Kirsimeti: Osinbajo ya ziyarci Buhari, ya bashi kyauta ta musamman

Osinbajo ya ziyarci Buhari, ya bashi kyauta ta musamman
Source: Twitter

Jajiberin Kirsimeti: Osinbajo ya ziyarci Buhari, ya bashi kyauta ta musamman

Osinbajo da Buhari
Source: Twitter

Jajiberin Kirsimeti: Osinbajo ya ziyarci Buhari, ya bashi kyauta ta musamman

Osinbajo ya ziyarci Buhari, ya bashi kyauta ta musamman a jajiberin Kirsimeti
Source: Twitter

Jajiberin Kirsimeti: Osinbajo ya ziyarci Buhari, ya bashi kyauta ta musamman

Osinbajo ya ziyarci Buhari, ya bashi kyauta ta musamman a jajiberin Kirsimeti
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel