Yanzu Yanzu: DSS ta saki Dasuki daga tsare shi da ta yi

Yanzu Yanzu: DSS ta saki Dasuki daga tsare shi da ta yi

- Tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro (NSA), Sambo Dasuki wanda ke tsare ya samu yanci bayan shekaru hudu da ya yi a tsare a hannun hukumar tsaro na farin kaya (DSS)

- Lauyan Dasuki, Mista Ahmed Raji (SAN) ne ya tabbatar da cigaban

- Gwamnatin tarayya ce ta bayar da umarnin sakin nasa

Tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki mai ritaya, wanda ke tsare ya samu yanci bayan shekaru hudu da ya yi a tsare a hannun hukumar tsaro na farin kaya (DSS).

Lauyan Dasuki, Mista Ahmed Raji (SAN), ya tabbatar da cigaban ga jaridar Vanguard.

Raji wanda ya yi magana a wayar tarho ya ce: “Eh an sake shi kuma yana shirin barin wajen.”

Da farko mun ji cewa Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin sakin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro (NSA), Sambo Dasuki, da kuma jagoran yunkurin gudanar da zanga-zanga a kasa, Omoyele Sowore.

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma aministan shari'a, Abubakar Malami, shine ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar da shi ranar Talata.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya kira Jonathan kan harin da yan bindiga suka kai Otuoke

Malami ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar bayar da umarnin sakinsu ne domin yin biyayya ga umarnin kotuna a kan bayar da belinsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel