Buhari ya kira Jonathan kan harin da yan bindiga suka kai Otuoke

Buhari ya kira Jonathan kan harin da yan bindiga suka kai Otuoke

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Talata, 24 ga watan Disamba ya kira tsohon shugaban kasa, Dr Goodluck Jonathan, don yi masa jaje kan harin da aka kai gidansa na Otueke a Bayelsa.

A cewar wani jawabi daga babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, Mallam Garba Shehu, shugaban kasar ya sake ba Jonathan tabbacin samun tsaro da dukkanin yan Najeriya.

Jawabin ya kuma yi jaje ga iyalan sojan da ya mutu da wanda ya jikkata a lokacin harin.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata, ya kira tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan domin yi masa jaje biyo bayan wani hari da yan bindiga suka kai gidansa da ke Otueke, jihar Bayelsa.

"A hiran wayan, Buhari ya nuna bakin ciki kan harin wanda a ciki wani hazikin soja ya rasa ransa.

“Yayinda ya ke yaba wa sojojin da ke aiki kan dakile harin da suka yi, Shugaban kasar ya yi ta’aziyya ga iyalai da jami’ai da dakarun sojin Najeriya kan rasa daya daga cikinsu da suka yi.

KU KARANTA KUMA: Mutane 2 sun mutu yayinda 13 suka jikkata a harin Maiduguri

“Shugaba Buhari ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da mayar da hankali wajen tsaron tsohon shugaban kasar da dukkanin al’umman kasa," cewar sanarwar.

A baya mun ji cewa a ranar Talata ne wasu 'yan bindiga suka kai hari gidan tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, da ke garin Otuoke a yankin karamar hukumar Ogbia, jihar Bayelsa.

Wasu majiya sun bayyana cewa sojojin dake gadi a gidan tsohon shugaban kasar sun dakile harin tare da kashe uku daga cikin 'yan bindigar yayin da suke kokarin shiga gidan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel