Cushe a kasafin kudi ya halatta - Shugaban majalisa

Cushe a kasafin kudi ya halatta - Shugaban majalisa

Kakakin Majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Y. Suleiman ya kaddamar da cewa cushe a kasafin kudi ya halasta tunda a kan yi hakan ne domin tabbatar da adalci da daidaito ga kowa.

Kakakin majalisar ya kaddamar da hakan a ranar Talata, 24 ga watan Disamba yayinda yake gabatar da kasafin kudin 2020 da aka amince dashi ga gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammed Abdulkadir domin aiwatar dashi bayan majalisar ta yi muhawara da amincewa dashi.

Abubakar Suleiman yayinda yake gabatarwar ya bayyana cewa, “a kokarin aiki kan kasafin da Gwamnan ya gabatar a ranar 10 ga wannan watan, mun mayar da wasu kudade zuwa ga wasu ma’aikatu, hakan shine abunda wasu ke kira da cushe, don haka, cushe halal ne.

Sai dai kuma ya bayyana cewa girman kasafin kudin da Gwamnan ya gabatar na nan a yadda yake, inda ya kara da cewa rabe-raben kasafin na nan yadda yake duk da gyare-gyaren da majalisar ta yi.

Sannan kakakin Majalisar ya ba gwamnan tabbacin cewa majalisar dokokin za ta cigaba da mara wa bangaren zartarwa baya wajen aiwatar da kasafin kudi da sauran tsare-tsaren da ke da kudirin kawo cigaban jihar don ta samu shiga tsara a kasar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kashe soja da wasu 3 yayinda yan bindiga suka kai hari gidan Jonathan

Daga nan Abubakar Suleiman ya gode na gwamnan kan sany hannu da gabatar da wasikun yabo ga dukkanin mambobin majalisar 31, cewa Wannan shine karo na farko da hakan ke faruwa tsakanin bangarorin biyu na gwamnati.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel