Mutane 2 sun mutu yayinda 13 suka jikkata a harin Maiduguri

Mutane 2 sun mutu yayinda 13 suka jikkata a harin Maiduguri

- Rahotanni sun kawo cewa an kashe akalla mutane sannan 13 suka jikkata a lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari tashar sojoji a arewa maso gabashin Najeriya

- An tattaro cewa mayakan na Boko Haram cikin manyan motoci 14 sun kaddamar da harin nasu kan sojoji a kauyen Maina da ke kusa da garin Biu

- Sai dai sojojin sun yi nasarar dakile harin bayan sun tursasa mayakan janye wa ta karfin tuwo

Akalla mutane biyu aka kashe sannan 13 suka jikkata a lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari tashar sojoji a arewa maso gabashin Najeriya, wani kakakin karamar hukumar da mazauna yankin suka bayyana a ranar Talata, 24 ga watan Disamba.

Mayakan Boko Haram a manyan motoci 14 sun kaddamar da wani hari kan sojoji a kauyen Maina da ke kusa da garin Biu, kilomita 180 daga kudu maso yammacin Maiduguri, babbar birnin jihar Borno.

An gano yan farin hula a lokacin musayar wuta da ya gudana na tsawon sa’o’i biyu da ya biyo baya.

“Mutane biyu sun mutu,” Bulama Talba, wani shugaban karamar hukuma a Borno ya bayyana a Wani jawabi, bayan ya ziyarci babban asibitin Biu inda ake kula da wadanda abun ya cika da su a ranar Talata.

“Mutane goma sha uku sun ji raunuka da dama sakamakon harbin bindiga a lokacin da suke kokarin tserewa,” inji Talba.

Sai dai mazauna yankin sun ce mutane uku daga ahli guda aka kashe a lokacin arangamar lokacin da roka ya tashi kusa da gidansu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kashe soja da wasu 3 yayinda yan bindiga suka kai hari gidan Jonathan

An tursasa wa yan ta’addan janyewa, cewar mayakin farin hula, Mustapha Karimbe.

“Babu rahoto kan wadanda suka mutu daga bangarorin biyu,” inji shi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel