Jonathan ya yi magana a kan harin da 'yan bindiga suka kai gidansa

Jonathan ya yi magana a kan harin da 'yan bindiga suka kai gidansa

A ranar Talata ne wasu 'yan bindiga suka kai hari gidan tsohon shugaban kasa, Goodluck Ebele Jonathan, da ke garin Otuoke a yankin karamar hukumar Ogbia, jihar Bayelsa.

Wasu majiya sun bayyana cewa sojojin dake gadi a gidan tsohon shugaban kasar sun dakile harin tare da kashe uku daga cikin 'yan bindigar yayin da suke kokarin shiga gidan.

Daya daga cikin majiyar, wacce ta nemi a boye sunanta, ta ce 'yan bindigar sun yi amfani da kananan jiragen ruwa masu gudu wajen zuwa gidan, kuma sun bude wa sojojin dake gadi a gidan wuta nan take.

A cikin wani jawabi da ya fitar a Abuja, kakakin Jonathan, Ikechukwu Eze, ya ce tsohon shugaban kasar ba ya gidan a lokacin da 'yan bindigar suka kai harin.

"Da safiyar ranar Talata ne wasu 'yan bindiga suka kai wa jami'an tsaron dake gadi a gidan tsohon shugaban kasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, hari," a cewar jawabin.

Duk da babu wanda ya samu rauni daga cikin jami'an tsaron dake gadi a gidan, mazauna garin suna zargin cewa an kai harin ne domin a kashe tsohon shugaban kasar.

Tun da farko, Legit.ng ta sanar da cewa an zargi ‘yan bindigar da suka kai hari gidan tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan da zuwa halaka shi. Hakan ya biyo bayan budewa sojojin da ke tsaron shingen dake gab da gidan Jonathan din ne dake Otueke.

Kamar yadda wani rahoton da Dr. Tubolayefa ya wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta tuwita, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun shirya tsaf ne don daukar ran tsohon shugaban kasar. Hakan ne kuwa yasa suka yi shiri tamkar sojojin da ke tsaron shingen gidan shugaban kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel