DSS: An turo wakili musamman daga Amurka saboda shari’ar Yele Sowore

DSS: An turo wakili musamman daga Amurka saboda shari’ar Yele Sowore

Kasar Amurka ta aiko da wani Wakili na musamman domin ya rika lura da yadda shari’ar gwamnatin tarayya da Omoyele Sowore za ta kasance.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Sahara Reporters, wannan Wakili da aka aiko, shi ne zai zama idanun kasar ta Amurka a wajen shari’ar.

An ga Marcus Thornton su na gaisawa a Ranar Litinin, 23 ga Watan Disamban 2019, da Femi Falana, wanda shi ne babban Mai kare Sowore a kotu.

Mista Thornton jami’in siyasa ne a ofishin jakadancin kasar Amurka da ke Najeriya. Zai halarci zaman kuliya ne domin ya ga yadda shari’ar ta ke gudana.

Ana shari’a tsakanin Yele Sowore da gwamnatin Najeriya ne a wani babban kotun tarayya da ke Abuja. A zaman jiyan Alkalin da ke sauraron karar ya janye.

KU KARANTA: Gwamnatin Tarayya ta bada umarni a fito da Sowore da Dasuki

DSS: An turo wakili musamman daga Amurka saboda shari’ar Yele Sowore

Alkali ya janye daga kara saboda Sowore ya taba zargin ya karbi cin hanci
Source: UGC

Idan ba ku manta ba, ‘Yan majalisar kasar Amurka kusan biyar su ka fito su na jan-kunnen gwamnatin Najeriya a kan sake kama ‘Dan gwagwarmayar.

A kwanakin bayan nan ma ‘Dan majalisar Amurka, Josh Gottheimer ya gana da Ope Sowore, wanda ita ce Mijin na ta ya ke tsare a hannun jami’an DSS.

An kama Omoyele Sowore ne a watan Agustan bana, bayan watanni hudu a tsare, aka bada belinsa. Kwatsam kuma sai aka sake yin ram da shi a cikin kotu.

Jim kadan da samun wannan labari sai mu ka ji cewa gwamnatin tarayya ta bada umarni a saki Yele Sowore da kuma Sambo Dasuki wanda ya dade a tsare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng News

Online view pixel