Ganduje da Sanusi: Ganduje ya kauce wa kwamitin sulhu, ya tafi Umrah

Ganduje da Sanusi: Ganduje ya kauce wa kwamitin sulhu, ya tafi Umrah

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya garzaya kasar Saudi Arabia don yin Umrah na makonni biyu. A yayin da gwamnan ya tafi Umrah, mataimakinsa Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ne zai zama mukaddashin Gwamnan. Ganduje ya yi umarni tare da kira ga ma'aikatu, bangarori da cibiyoyin gwamnatin jihar da su ba mukaddashin gwamnan hadin kai.

Wannan na kunshe ne a takardar da sakataren yada labarai na Gwamnan, Abba Anwar ya fitar a ranar Litinin kuma ya aikewa da jaridar Solabace.

Idan zaku tuna, zauren dattijan Arewa sun garzaya jihar Kano din don sasanci tsakanin Abdullahi Ganduje da Sarki Sanusi a jihar Kano din a ranar Lahadi. Dattijan suna tattaunawa ne da masu ruwa da tsaki a jihar don samun shawo kan matsalar da ke tsakanin gwamnan da basaraken.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Gwamnoni sun bukaci a kara duba yanayin kasafin kudin shiga

Hakazalika, wani kwamiti mai karfin gaske da Shugaba Buhari ya aike zuwa Kano din don sasanta tsakanin gwamnan da basaraken, ya samu shugabancin tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Abdussalami Abubakar. Tuni kuwa suka fara tattaunawa da gwamnan tare da sarkin.

Amma kuma, majiyoyi da dama sun sanar da jaridar Solacebase cewa, Ganduje ya sanar da kwamitin da ya samu shugabancin Abdulsalami cewa, ya zama wajibi ya garzaya Umrah din nan kamar yadda ya tsara. Ya sanar da hakan ne ta bakin shugaban Gwamnonin Najeriya, Dr. Kayode Fayemi.

Hakazalika, kwamitin ya bukaci ganin gwamnan a Kano amma kamar yadda majiyar ta sanar, ya ce hakan ba zai yuwu ba amma zai samu tsohon shugaban kasar Najeriya din a Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel