Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin sakin Dasuki da Sowore

Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin sakin Dasuki da Sowore

- Bayan shafe fiye da shekaru biyar a tsare, Sambo Dasuki, tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, zai shaki iskar 'yanci

- Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin a saki Dasuki tare da matashin nan da ya yi yunkurin jagorantar zanga-zangar juyin - juya hali, Omoyele Sowore

- Abubakar Malami, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma aministan shari'a, ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar ranar Talata

Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin sakin tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro (NSA), Sambo Dasuki, da kuma jagoran yunkurin gudanar da zanga-zanga a kasa, Omoyele Sowore.

Babban lauyan gwamnatin tarayya kuma aministan shari'a, Abubakar Malami, shine ya sanar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar da shi ranar Talata.

DUBA WANNAN: Zamfara: Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP ya koma APC

Malami ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yanke shawarar bayar da umarnin sakinsu ne domin yin biyayya ga umarnin kotuna a kan bayar da belinsu.

"Muna kira garesu da su kasance masu biyayya ga sharudan da aka bayar da belinsu a kai, sannan su guji aikata duk wani abu da kan iya zama ya saba wa doka da tsaro domin za a cigaba da tuhumarsu a gaban kotu bisa dokokin kasa," a cewar Malami.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel