'Yan bidiga sun zo kashe Jonathan ne - Dr. Tubo

'Yan bidiga sun zo kashe Jonathan ne - Dr. Tubo

‘Yan bindigar da suka hari gidan tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan an zargesu da zuwa halaka tsohon shugaban kasar. Hakan ya biyo bayan budewa sojojin da ke tsaron shingen dake gab da gidan Jonathan din ne dake Otueke.

Kamar yadda wani rahoton da Dr. Tubolayefa ya wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta tuwita, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun shirya tsaf ne don daukar ran tsohon shugaban kasar. Hakan ne kuwa ya sa suka yi shiri tamkar sojojin da ke tsaron shingen gidan shugaban kasar.

Kamar yadda ya wallafa, “Yan bindigar da suka hari gidan Jonathan sun je kashesa ne. Muna godiya ga Ubangiji da basu tarar dashi a gida ba. Sun yi shiri ne tamkar sojojin da suke tsaron gidansa. Sunyi musayar wuta har suka hallaka soja daya. Sauran sojojin sun yi amfani da sulkensu don kare kansu, amma da asarar rayukan sai ta fi haka.

DUBA WANNAN: Abun da yasa muke yi wa jama'a rijista - Gwamnatin jihar Kaduna

Abun dadin shine yadda Goodluck bai koma Otueke ba saboda wani karamin dalili. Ya dage komawarsa ne zuwa yau, da wadannan mutanen sun tarar da shi. Mun gode Ubangiji da bai basu nasarar cimma burinsu ba.”

A safiyar yau ne wasu ‘yan bindiga suka hari gidan tsohon shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan. Soja daya ya rasa rayuwarsa yayin musayar wutar da ta wakana tsakanin ‘yan bindigar da sojojin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel