Yanzu Yanzu: An kashe soja da wasu 3 yayinda yan bindiga suka kai hari gidan Jonathan

Yanzu Yanzu: An kashe soja da wasu 3 yayinda yan bindiga suka kai hari gidan Jonathan

- Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani soja da ke aikin gadi a gidan tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda ke kusa da kogi a Otuoke

- An tattaro cewa sojojin wadanda suka dakile yunkurin yan ta’addan na shiga gidan sun kashe mutane uku cikin yan bindigan

- Wata majiya wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ce yan bindigan sun shigo ta kogin a cikin jirgin ruwa sannan suka bue wuta kan sojojin

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe wani soja da ke aikin gadi a gidan tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda ke kusa da kogi a Otuoke, karamar hukumar Ogbia da ke jihar Bayelsa.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa sojojin wadanda suka dakile yunkurin yan ta’addan na shiga gidan sun kashe mutane uku cikin yan bindigan.

Daya daga cikin majiyoyin, wacce ta nemi a sakaya sunanta, ta ce yan bindigan sun shigo ta kogin a cikin jirgin ruwa sannan suka bue wuta kan sojojin.

Majiyar ta ce: "Yan bindiga wadanda suka zo a jiragen ruwa biyar sun kai hari gidan tsohon shugaban kasa Jonathan.

"An kashe wani jami'in tsaro da ke aiki da tsohon shugaban kasar sannan an harbe kimanin yan bindiga uku."

Wani jigon matasan Ogbia, wanda ya nemi a boye sunansa, ya bayyana harin da aka kai gidan Jonathan a matsayin abun damuwa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Ministan Buhari ya dakatar da shugabar REA

Ya kuma bayyana cewa sojojin, wadanda tashar su ke a wajen kogin, sun dakile harin amma abun bakin ciki daya daga cikinsu ya mutu a cikin hakan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel